‘Yan Bindiga Sun Kona Ofishin ‘Yansanda, Coci Tare Da Garkuwa Da Waus A Neja
Wasu mutane dauke da makamai da ake zargin ‘yan bindiga ne, a safiyar Lahadi, sun kona ofishin ‘yansanda da cocin UMC a garin Sokombara da ke karamar hukumar Agwara ta jihar Neja.
LEADERSHIP ta tattaro cewa ‘yan bindigar sun kuma kashe wata tsohuwa, sun sace mutane biyar daga cikin al’ummar sannan suka sace kayan abinci da sauran kayayyaki na mutanen kauyen.
- Akwai Matsala Kasafin Ilimi Ya Tsaya Kashi 6 Zuwa 7 Tsawon Shekara Biyar —Masana
- Yadda Ake Kamuwa Da Ciwon Koda
Da yake tabbatar wa LEADERSHIP lamarin, jami’in hulda da jama’a na ‘yansandan (PPRO), SP Wasiu Abiodun, ya ce; “‘Yan bindiga dauke da makamai sun mamaye al’ummar Agwara, sun kai hari ofishin ‘yansanda inda jami’an suka yi artabu da su, daga nan sai ‘yan bindigar suka harbo abun fashewa a kan ofishin, bayan sun yi galaba a kan jami’an.”
“Daga baya ‘yan ta’addan sun koma cocin UMC da ke cikin al’ummar, suka kona wani bangare na cocin, sannan suka nufi wasu yankuna, inda suka sace kimanin mutane biyar wadanda har yanzu ba a tantance su waye ba.”
LEADERSHIP ta tuna cewa, sabon harin yana cikin manyan hare-hare guda uku da aka kai wa al’ummomin Agwara tun bayan sacewa da sakin yaran makaranta da ma’aikata na Papiri a ƙarshen 2025 a wannan ƙaramar hukumar ta Agwara da ke jihar.