Ta’addanci: Borno na cikin mummunan hatsari — Ndume




Tsohon Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, ya yi gargaɗin cewa wasu sassan Jihar Borno na iya komawa ƙarƙashin ikon ’yan ta’adda idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba.

Ndume, wanda ke wakiltar Borno ta Kudu, ya faɗi haka ne yayin wata ganawa da manema labarai a Abuja.

Ya ce babban abin da ke hana sojoji samun nasara shi ne rashin isassun makamai da kayan aiki.

Ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙarfafa rundunar sojoji da makamai na zamani da kuma wadatattun alburusai domin su iya yaƙar ’yan ta’adda yadda ya kamata.

Sanatan ya yi wannan kira ne bayan wata ziyara da ya kai garuruwan Ngoshe da Pulka tare da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, bayan hare-haren da aka kai kwanan nan, inda aka rasa rayuka da dukiyoyi.

Rahotanni sun nuna cewa mayaƙan Boko Haram sun kai hari Ngoshe da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza, inda suka kashe sojoji, shugaban ƙauye da wasu dattawa, sannan suka sace mata da yara.

Ko da yake daga baya sojoji sun sake ƙwato yankunan, Ndume ya ce sun fuskanci matsaloli sosai kafin hakan.

“An sanar da ni cewa sojojinmu sun janye ne saboda ƙarancin alburusai, har sai da aka tura musu ƙarin dakaru kafin a samu nasarar dawo da yankunan. Abin takaici, babu abin da ya rage a waɗannan garuruwa face ɓarna,” in ji shi.

Ndume, ya yaba wa Gwamna Zulum kan yadda yake ziyartar waɗanda abin ya shafa da kuma ’yan gudun hijira, yana mai cewa hakan na ƙarfafa musu gwiwa.

Sai dai ya ce dole ne Gwamnatin Tarayya ta gaggauta shiga tsakani domin sake gina yankunan da aka lalata da kuma taimaka wa mutanen da suka rasa gidajensu.

“Na ga irin ɓarnar da aka yi a Ngoshe abin ya wuce misali. Komai ya lalace ƙwarai, sai ƙaramin masallaci kaɗai ya rage.

“Duk da haka, mutanen yankin suna da juriya, kuma gwamnati na ƙoƙarin farfaɗo da yankin. Amma dole ne Gwamnatin Tarayya ta gaggauta ɗaukar mataki,” in ji Ndume.

A ƙarshe, Ndume ya ce zai haɗa kai da sauran Sanatoci domin ganin an samar da tallafin da ya dace, yana mai fatan za a ɗauki matakan gaggawa kafin lamarin ya ƙara tsananta.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *