Shin Michael Carrick Ne Kocin Da Manchester United Ta Shekara 13 Tana Nema?

[ad_1]

Tun bayan barin Sir Alex Ferguson a shekarar 2013, ƙungiyar ƙwallon kafa ta Manchester United ta kasa samun koci da zai daidaita harkokin ƙungiyar tare da dawo da martabarta a matakin kololuwa. A tsawon wannan lokaci, ta ɗauki manyan masu horarwa da dama ciki har da David Moyes, da Louis van Gaal, da Jose Mourinho, da Ole Gunnar Solskjaer, da Ralf Rangnick, da Erik ten Hag da kuma Ruben Amorim, amma duk da haka ba su samu damar kafa ƙungiyar kamar yadda take a Old Trafford da ba.

A baya-bayan nan ne United ta sallami Ruben Amorim, wanda bai kai ko shekara guda a matsayin koci ba, sannan ta miƙa ragamar riƙon ƙwarya ga tsohon ɗan wasanta, Michael Carrick. Yanzu haka Manchester United na matsayi na hudu a teburin gasar Firimiya da maki 38, inda take gaba da ƙungiyoyi irinsu Liverpool da Chelsea, lamarin da ya jawo hankalin masoya da masu sharhi.

  • Shin Michael Carrick Zai Iya Dawo Da Manchester United Hayyacinta
  • Tsaro: Gwamnatin Nijeriya Ta Ɗauki Rayukan Mutane Da Muhimmanci – Peter Obi

Carrick ya fara aikinsa da nasarori masu armashi, inda ya jagoranci United a wasanni biyu masu nauyi da Manchester City da Arsenal, inda ya samu nasara a duka biyun. Ciki har da doke Arsenal da ci 3-2 a filinsu, sannan ya doke Manchester City ƙarƙashin jagorancin Pep Guardiola a Old Trafford, abin da ya sa United ta samu nasara biyu a jere bayan dogon lokaci.

Duk da cewa Carrick na matsayin kocin riƙon ƙwarya ne, kuma ƙungiyar na ci gaba da lalubo kocin dindindin, amma nasarorin da ya samu sun sa magoya baya da masu fashin baƙi ke hasashen ko shi ne kocin da Manchester United ta shafe tsawon shekaru 13 tana nema domin dawo da martabar ƙungiyar da ta lashe gasar Firimiya sau da dama a tarihinta.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *