Masu bin Abba zuwa APC za su dawo NNPP — Sanata Hanga

[ad_1]



Sanatan Kano ta Tsakiya Rufa’i Sani Hanga, ya bayyana cewa waɗanda suka sauya sheƙa daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC a jihar da kansu za su dawo, saboda matsalar da za su fuskanta a APC.

Sanata Hanga ya bayyana ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf, daga jam’iyyar NNPP a matsayin ƙundunbalar siyasa da ba za ta kai shi ya baro.

Gwamnan tare da wasu ’yan majalisar dokokin jiha da kuma wasu masu riƙe da mukaman siyasa sun sanar da ficewarsu daga NNPP, suna danganta hakan da rikice-rikicen cikin gida da kuma sabanin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar.

A tattaunawarsa da wakilinmu a ranar Lahadi, Sanata Hanga ya ce ya taɓa gargadin gwamnan kan kada ya yi hakan, amma bai saurare shi ba.

“Da na ji labarin, na je na yi masa nasiha kada ya ɗauki wannan matakin da zai kai shi ya baro, amma bai ji ba. Gaskiya ban san abin da ya faru ba,” inji shi.

Sanatan ya yi hasashen cewa da dama daga cikin muƙarraban gwamnan da suka bi shi zuwa APC za su dawo NNPP.

“Yawancinsu za su dawo, domin zuciyarsu tana tare da mu, kuma ba su da inda za su je,” ya kara da cewa.

Hanga ya jaddada cewa masu barin jam’iyyar da ke da burin siyasa za su dawo daga bisani, domin damar samun nasara ba a NNPP ba, zai yi musu wuya.

Ya ce gwamnan ma kansa zai yi wuya ya samu tikitin takara a sabuwar jam’iyyar da ya shiga.

“Ba a ba da tikitin takara kai tsaye. Duk wanda yake son tsayawa dole ya shiga zaɓen fidda gwani, kuma ina shakku ko zai iya lashewa. Idan ya gwada, za su kayar da shi,” inji Hanga.

Sanatan ya bayyana takaici matuƙa kan abin da ya kira cin amana, yana mai tunawa da yadda gwamnan ya yi tafiyar siyasa tun daga matakin farko ƙarƙashin jagorancin shugaban NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

“Shi ne ya ɗauke shi daga kasa ya kai shi inda yake a yau. Amma yanzu ya bar shi ya koma jam’iyyar da ta yi mana adawa da kuma wulakanci, abin takaici ne. Mun bar shi da tafiyarsa, amma wannan sauya sheƙa zai yi masa illa sodai a siyasa,” in ji Hanga.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *