Gwamnatin Jihar Borno Za Ta Dawo Da ‘Yan Gudun Hijira 3,000 Daga Kamaru

[ad_1]

Gwamnatin Jihar Borno, ta kammala shirye-shiryen mayar da ‘yan gudun hijira ‘yan Najeriya sama da 3,000 daga Kasar Kamaru zuwa gidajensu, bisa radin kansu bayan shekara 11.

Wannan, a cewar sanarwar da kakakin gwamnan Jihar Borno, Malam Dauda Iliya, ya yi na cika alkawarin da Gwamna Zulum ya yi na mayar da daukacin ‘yan gudun hijirar Nijeriya daga Borno, da ke ma-kwaftaka da Chadi, Kamaru da kuma Nijar sama da shekara 11.

  • Dambarwar Da Ta Biyo Bayan Sauya Sheƙar Gwamna Yusuf Na Jihar Kano
  • Raheem Sterling Ya Bar Chelsea Bayan Shafe Shekaru 3

Ya ce, a ziyarar da ya kai sansanin a watan Disambar 2025, Gwamna Zulum ya tabbatar wa ‘yan gudun hijirar da ke son komawa gida cewa; za su yi hakan cikin aminci da mutunci.

Iliya ya kara da cewa, a lokacin zaman nasu, hukumomin Kamaru da abokan huldar jin kai, sun ba su matsuguni, kiwon lafiya, ilimi da sauran muhimman ayyuka. An kuma ware wa ’yan gudun hijira da da-ma filayen noma, don tallafa wa ayyukan noma, rage dogaro da agaji da kuma ba su damar ci gaba da kula da iyalansu cikin kwanciyar hankali.

Wakilbe ya ce, “Saboda ingantaccen tsaro a sassa da dama na Borno da kuma kokarin sake gina jihar da ake yi, ‘yan gudun hijira da dama sun bayyana aniyarsu ta komawa gida, bisa radin kansu.”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *