An Kaddamar Da Aikin Samar Da Fitilu Kan Titi Masu Aiki Da Hasken Rana A Bujumbura Na Burundi Bisa Tallafin Sin
[ad_1]
A daren ranar Juma’ar da ta gabata ne aka gudanar da bikin kaddamar da fitilu kan titi masu aiki da hasken rana a babbar hanyar Mao Zedong mai tsawon kilomita 1.2, dake birnin Bujumbura cibiyar kasuwancin kasar Burundi, aikin da kasar Sin ta tallafa wajen gudanar da shi.
Manyan jami’an kasar Burundi sun bayyana aikin a matsayin wanda ya dace da manufar kasar ta bunkasa cin gajiya daga makamashi mai tsafta, da inganci, da samar da ci gaba mai dorewa. Fitilun wadanda yawansu ya kai 101, an kafa su ne reras a kan titin Mao Zedong, darke gundumar Mukaza ta birnin na Bujumbura. Suna kuma aiki da haske rana, tare da kunnunawa da mutuwa da kansu, gwargwadon yanayin dare da hasken rana.
Game da hakan, gwamnatin Burundi ta bayyana matukar godiyarta ga kasar Sin, bisa agajinta na ganin an cimma nasarar kammala aikin. A jawabinsa yayin bikin kaddamar da aikin, babban sakatare a ma’aikatar raya makamashi, da hakar ma’adanai, da raya masana’antu, da cinikayya da yawon bude ido ta kasar Burundi Martin Ndayizeye, cewa ya yi wannan aiki mai kunshe da fasahohin zamani, kuma na cin gajiya mai dorewa, muhimmin mataki ne na zamanantar da birnin Bujumbura.
Ndayizeye, ya kara da jinjinawa kasar Sin, bisa kasancewarta sahihiyar kawa bisa manyan tsare-tsare ga kasar Burundi. Ya ce wannan babban goyon baya, na nuni ga kyakkyawan yanayin hadin gwiwa, da kawance dake wakana tsakanin kasashen biyu.
Tun a shekarar 1978 ne majalisar birnin Bujumbura, ta sanyawa daya daga manyan titunan birnin sunan Mao Zedong, domin karrama gudummawar da shugaba Mao ya baiwa yunkurin neman ‘yancin kan kasashen Afirka, da kuma martaba abotar Sin da kasar Burundi. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link