Maigadi ya kashe abokin aikinsa a Gidan Gwamnatin Gombe
Wani ma’aikaci da ke aiki a Gidan Gwamnatin Jihar Gombe, mai suna Shuaibu Adamu, ya kashe abokin aikinsa Malam Umar.
Marigayin, wanda aka fi sani da Baba Usama, yana aiki a Gidan Gwamnatin a matsayin mai kula da rijiyar burtsatse.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an tarar da Malam Umar kwance babu rai a harabar Gidan Gwamnatin.
An ɗaure wuyansa da mazariyar wandonsa sannan an saka wani abu aka rufe bakinsa.
DSP Abdullahi, ya ce ’yan sanda sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 3:50 na yammacin ranar Juma’a, 26 ga watan Disamba.
An garzaya da marigayin zuwa Asibitin Ƙwararru na Gombe, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.
Daga nan aka ajiye gawarsa a ɗakin ajiyar gawarwaki na asibitin domin yin bincike.
Bayan faruwar lamarin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Umar Ahmed Chuso, ya kai ziyara wajen da abin ya faru tare da bayar da umarnin gudanar da bincike.
Binciken ’yan sanda, ciki har da duba na’urar CCTV a harabar Gidan Gwamnatin, ya nuna wani matashi mai shekara 19, Shuaibu Adamu, wanda aka fi sani da Yaya Mama, an gan shi yana dukan marigayin kafin rasuwarsa.
Shuaibu ma’aikacin tsaro ne na wucin gadi a wani kamfanin gine-gine da ke gudanar da ayyuka a cikin Gidan Gwamnatin.
’Yan sanda sun ce bayan faruwar lamarin, wanda ake zargi ya tsere, amma daga bisani aka gano inda yake tare da kama shi da misalin ƙarfe 11 na daren ranar, a maɓoyarsa da ke unguwar Bagadaza a birnin Gombe.
DSP Abdullahi, ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa a yayin gudanar da bincike.
A halin yanzu yana tsare a hannun ’yan sanda, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano cikakken bayani kafin gurfanar da shi a gaban kotu.