Majalisar Wakilai Ta Gayyaci CBN Da Bankuna Kan Cire Wa Kwastomomi Kudi Ba Dalili
[ad_1]
Majalisar Wakilai ta kira Babban Bankin Nijeria (CBN) da manyan bankunan kasuwanci domin su bayyana dalilin yawaitar cire kuDi daga asusun kwastomomi ba tare da wani bayani ba a fadin kasar.
Wannan mataki ya biyo bayan amincewa da wani kudurin gaggawa na kasa da Hon. Tolani Shagaya (APC, Kwara) ya gabatar yayin zaman majalisar a ranar Talata.
Shagaya ya bayyana damuwa kan abin da ya kira “yawan caje-caje marasa iyaka, da kuma wadanda ba a bayyana dalili ba” da bankuna ke kakaba wa kwastomomi, duk da kasancewar dokokin CBN da ke tsara yadda ake biyan kudin sabis na kudi.
Ya bayyana cewa duk da cewa ana sa ran bankuna za su bayar da ayyuka cikin gaskiya da farashi mai adalci, yawancin kwastomomi na ci gaba da fuskantar yawan cire kudi daga asusunsu ciki har da kudin sakon SMS, kudin katin ATM da kula da asusu, kudin canja kudi, kudin haraji (stamp duty), da wasu cajin da ba a bayyana ba, wanda a wasu lokuta ana maimaita su ko kuma ba su da hujja.
Shagaya ya ce: “Wadannan hanyoyin da bankuna ke amfani da su wajen zaluntar kwastomomi na fiye da kima suna shafar ‘yan kasuwa, masu karamin karfi, dalibai da kuma kungiyoyin da ke cikin mawuyacin hali a wannan yanayin tattalin arziki mai tsanani. Idan ba a gudanar da bincike da daukar mataki cikin gaggawa ba, wannan matsala za ta ci gaba da rage amincewar jama’a ga tsarin banki tare da lalata kokarin shigar da jama’a cikin tsarin hada-hadar kudi.”
Bayan amincewa da kudurin, Majalisar Wakilai ta umurci CBN da ta wallafa jerin caje-cajen da aka amince da su cikin sauki, tare da kakabawa bankunan da suka saba dokoki hukunci mai tsanani.
‘Yan majalisar sun kuma bukaci babban banki ya kafa wata hanyar karbar koke-koke wacce za ta kasance mai saukin amfani da inganci ga kwastomomi da abin ya shafa daga cajin da ba bisa ka’ida ba ko masu yawa.
Haka kuma, Majalisar ta umurci Hukumar Kula da Gasar Kasuwa da Kare Hakkin Masu Amfani (FCCPC) da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da kamfe na wayar da kan jama’a a fadin kasa don ilmantar da ‘yan Nijeria game da hakkokinsu dangane da cajin banki.
An ba kwamitocin da ke kula da Dokokin Banki da Hukumomin Banki aikin gudanar da cikakken bincike tare da mika rahoto cikin makonni hudu don daukar mataki na gaba a majalisa.
[ad_2]
Source link