Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Wanda Aka Sace A Kan Iyakar Kano da Katsina
[ad_1]
Dakarun rundunar hadin gwiwa (JTF) Faruruwa sun fatattaki masu garkuwa da mutane tare da ceto wani wanda aka yi garkuwa da shi a lokacin wani samame da suka kai da sanyin safiyar yau a kan iyakar Kano da Katsina.
An gudanar da wannan samamen ne da misalin karfe 1 na dare a ranar Lahadi, 28 ga Disamba, 2025, bayan samun bayanan sirri daga rundunar tsaro ta ‘yansanda (FOB) Yankwada game da tahowar ‘yan bindigar daga yankunan Daurawa da Kira na jihar Katsina zuwa yankin Kano.
- Tsaro: Yadda Gwamnoni Ke Kafa Rundunonin Tsaro A Jihohinsu
- Mutane 9 Sun Mutu Bayan Fashewar Jerin Bama-bamai A Zamfara
A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar sojojin Nijeriya ta 3 Birget, Kaftin Babatunde Zubairu ya fitar, nan take aka tura jami’ai zuwa yankin kan iyaka. Sojojin sun yi arangama da ‘yan bindigar a Ungwan Dogo da Ungwan Tudu, inda aka yi musayar wuta mai tsanani.
Kaftin Zubairu ya ce, kwarewar rundunar sojojin ya tilasta wa ‘yan bindigar ja-da-baya cikin ruɗani zuwa yankin karamar hukumar Matazu ta jihar Katsina.
A yayin arangamar, an ceto wani wanda aka yi garkuwa da shi, mai suna Rabiu Alhaji Halilu, mai shekaru 38.
An kai Halilu, wanda ya samu rauni a ƙafarsa, zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta JTF Faruruwa, inda yake samun kulawar lafiya a halin yanzu.
Sojojin sun kuma gano babura biyu da ‘yan bindigar suka gudu suka bari, da kuma wasu shanu da ba a bayyana adadinsu ba da ake zargin na sata ne.
Kaftin Zubairu ya kara da cewa, sojojin suna cikin shirin ko-ta-kwana kuma suna ci gaba da gudanar da sintiri a yankin don tabbatar da tsaron lafiyar mazauna kan iyakar Kano da Katsina.
[ad_2]
Source link