Mutane 9 Sun Mutu Bayan Fashewar Jerin Bama-bamai A Zamfara


Akalla mutane tara sun mutu sakamakon fashewar bama-bamai a kan titin Dansadau a jihar Zamfara.

Fashewar ta faru ne a ranar Asabar a kusa da Mai Aya-aya, kafin mahadar Kwankelai a tsohon titin Dangulbi, kusa da kauyen Ruwan Dawa da Magamin Maitarko.

  • AFCON 2025: Nijeriya Ta Kai Zagayen ‘Yan 16 Bayan Doke Tunisia
  • Tsaro: Yadda Gwamnoni Ke Kafa Rundunonin Tsaro A Jihohinsu

Ana zargin cewa ‘yan bindiga ne suka dasa bama-baman (IEDs) a wurare uku daban-daban.

Wani ganau, Malam Yunusa Isah, mazaunin kauyen Malele, ya ce fashewar farko ta kashe mutane hudu a nan take.

Ya kara da cewa, fashewar ta biyu, ta afku ne lokacin da wata tirela ta taka bam ɗin, inda ya kashe mutane biyar nan take.

Wani mazaunin garin, Mal. Nuhu Ibrahim Dansadau, ya ce fashewar bama-baman guda biyu sun yi sanadiyyar mutuwar mutane tara, yayin da ake ci gaba da tattara bayanan wadanda suka mutu sakamakon fashewar bam ɗin na uku.

A halin yanzu, rundunar ‘yansandan jihar Zamfara ta tabbatar da cewa, ana zargin fashewar wasu abubuwa a kan titin Dansadau zuwa Magami amma ta ce ba a tantance ainihin adadin wadanda suka mutu ba tukuna.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yansanda, DSP Yazid Abubakar, ya ce ana ci gaba da bincike.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *