Jimillar Masu Tafiye-Tafiye Ta Jirgin Kasa A Bikin Sabuwar Shekara Ta Kai Miliyan 48 A Kasar Sin

[ad_1]

Kamfanin jirgin kasa na kasar Sin ya ba da labari a yau Lahadi cewa, a bikin murnar sabuwar shekara ta 2026 wato bikin Yuandan tsakanin ranekun1 zuwa 3 ga watan nan da muke ciki, jiragen kasa na kasar sun yi jigilar fasinjoji miliyan 48.087. Daga cikinsu, a ranar 1 ga Janairu, jiragen kasa na kasar sun yi jigilar fasinjoji miliyan 18.56, inda aikin jigilar yake tafiya cikin kwanciyar hankali.

A lokacin shirin raya ci gaban kasar Sin da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 14, nisan layin dogo na kasar Sin ya karu daga kilomita dubu 146.3 zuwa kilomita dubu 165, wanda ya karu da kashi 12.8%, yayin da layin dogo masu saurin gudu ya karu daga kilomita dubu 37.9 zuwa kilomita dubu 50.4, wanda ya karu da kashi 32.98%. Hakan ya bayyana cewa, Sin ta gina babban tsarin jirgin kasa mafi girma kuma na zamani a duniya wanda ya fi na kowace kasa ci gaba.

A cikin wa’adin shirin karo na 15, kamfanin jirgin kasa na kasar Sin zai gaggauta aikin shimfida hanyoyin jirgin kasa. Ya zuwa shekara ta 2030, tsawon layin dogon na kasar da za a yi da su zai kai kimanin kilomita dubu 180, ciki har da layin dogo mai saurin gudu kimanin kilomita dubu 60, kuma daga cikinsu layin dogon dake iya kaiwa da kawowa da kuma masu amfani da lantarki ya kai kashi 64% da 78% bi-da-bi, matakin da ya inganta karfin layin dogon kasar Sin. Dadin dadawa, tsarin babban jiragen kasa masu saurin gudu zai kara karfin kaiwa wurare daban-daban na kasar, inda za a samu karin kayayyaki na hanyoyin sufuri sosai, kana za a kusan gina babban tsarin jiragen kasa na zamani da ya amsa sunansa a duniya. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *