Ko Kin San…Amfanin Hulba Guda 21 Ga Lafiyar Dan Adam?
Daga Bilkisu Tijjani Kasim
…Ci gaba daga makon da yagaba ta
18. Ana amfani da Hulba don maganin kaikayin gaba; Yadda za a yi shi ne, a samu Hulba a haya da gishiri a dafa sannan a jira ya huce yadda ba zai yi lahani ga jiki ba, sai a zauna a ciki, zuwa wani lokaci, a kalla dai a samu minti 30 a cikin wannan ruwan Hulba. Haka za a yi har a samu waraka. Idan kina bukata za ki iya hada shayin Hulbar kina sha, ko kuma bayan kin dafa da gishirin, bayan kin debi ruwan da za ki zauna sai ki rage wani, ki jefa tsamiya ki sha.
19. Hulba na taimakawa matar dake fama da bushewar gaba; Ga matan dake fama da matsalar bushewar gaba, sai su samu man ridi su ke zubawa a cikin ruwan dumi sai su zauna a ciki, sannan daga bisani sai su rika yin matsi da Hulba, in sha Allahu za a dace.
20. Hulba na maganin ciwon ciki bayan haihuwa
21. Ana amfani da Hulba don gyaran mama; Bincike ya tabbatar da cewa ana amfani da Hulba don gyaran mama.
22. Abubuwan da ake bukata su ne; garin Hulba da garin Shammar da kuma zuma.
Yadda za a hada:
Za a samu garin Hulba da garin shammar. Ki debi cikin karamin cokalin guda daya na garin Hulbar sai a zuba cikin kofi mai tsafta, sannan a zuba garin shammar, shima cikin karamin cokali guda, sai a gauraye su waje guda, daga nan a dafa ruwa idan ya tafasa sai a kwara a kan garin Hulba da na shammar dake cikin kofin a juya su da cokali, bayan haka sai a rufe kofin. Bayan kamar minti 10 sai a tace da rariya, bayan an tace, sai a kawo zuma mai kyau a zuba a sha.
Bayan nan sai a shafa man Hulba a kai. Wajen shafawa akan a tabbatar an murza man sosai akan gaba daya yadda zai shiga fatar da kyau. Za a sha wannan hadin sau biyu a rana, wato da safe da kuma dare, kuma duk lokacin da aka kammala shan shayin haka nan za a shafa man Hulbar a kan, shi ma ya zama sau 2 kenan.
Yadda za ki gane maganin na amfani shi ne, ta hanyar jin kin yi nauyi, alamar yana amfani. Allah Ya sa mu dace, amin.