Boko Haram sun kashe gomman mutane da sojoji a ƙauyen Borno

[ad_1]



Ana zargin mayaƙan Boko Haram sun kai hari ƙauyen Darul Jamal da ke Karamar Hukumar Bama, a Jihar Borno, inda suka kashe gomman mutane da sojoji.

Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na daren ranar Juma’a.

Mutane da hukumomin tsaro sun tabbatar da aukuwar harin.

A kwanakin baya, Gwamnan Jihar, Babagana Umara Zulum, ya mayar da wasu mutane ƙauyen.

Shekaru da dama suna zaman ’yan gudun hijira a sansanoni daban-daban kafin a dawo da su.

Wani daga cikin mazauna yankin ya ce: “Rana ce mai matuƙar baƙin ciki. Ɗana da ɗan uwana sun mutu.

“Mun kirga gawarwaki 63 kuma mutane da dama sun jikkata. An tafi da wasu zuwa asibitoci a Maiduguri, yayin da wasu ke karɓar magani a Bama.”

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun ƙone gidaje da motoci.

Yawancin kashe-kashen sun faru ne a kusa da makarantar da ’yan gudun hijira, tashar mota, da kuma gidaje.

Wani mazaunin yankin ya ce maharan sun kai harin cikin shiri, inda suka kai farmaki wuraren da mutane suka taru.

Sun buɗe wa ’yan gudun hijira, ma’aikata, direbobi, da jami’an tsaro wuta.

Ya ƙara da cewa ’yan ta’addan ba sa son mutane su zauna a garin, shi ya sa suka kai harin.

Hukumomi har yanzu suna faɗi adadin waɗanda suka rasu, yayin da wasu da suka ji munanan raunuka ke rasuwa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *