Akwai cushe a dokokin harajin Tinubu – Dan majalisa

[ad_1]



Ɗan Majalisar Wakilai, Abdulsammad Dasuki (PDP, Sakkwaku) ya yi zargin cewa akwai banbance-banbance tsakanin dokokin harajin da Majalisar Dokoki ta amince da su da kundin da aka wallafa wa jama’a.

Dasuki, wanda ya yi magana ƙarƙashin Dokar Majalisa ta Shida a zauren majalisar ranar Laraba, ya shaida wa majalisar cewa abin da aka wallafa a kundin bai dace da abin da ’yan majalisa suka tattauna, suka kada kuri’a, suka kuma amince da shi ba.

A cewarsa, bayan amincewa da kudirin dokokin haraji, ya ɗauki lokaci a cikin kwanaki uku da suka gabata ya yi nazari sosai kan kwafin da Majalisar ta amince da shi da kuma nau’in da aka daidaita wanda majalisun biyu suka amince da shi, sai ya gano banbance-banbancen.

“Na kasance a nan, na ba da kuri’ata kuma an ƙirga ta, amma yanzu ina ganin wani abu daban gaba ɗaya,” in ji Dasuki, yana cewa ya samu kwafin dokokin da aka wallafa daga Ma’aikatar Bayani, inda ya gano cewa ba su yi daidai da abin da Majalisun suka amince da shi ba.

Ɗan majalisar ya jaddada cewa batun ba na gabatar da ƙudiri ba ne, sai dai na jawo hankalin majalisar kan abin da ya bayyana da “karya tsari” na aikin majalisa da kundin tsarin mulki.

Ya roƙi Kakakin Majalisa da ya tabbatar dukkan takardun da suka dace, ciki har da nau’in da aka daidaita da kuma kwafin da aka fitar da ke yawo a halin yanzu, su zo gaban Kwamitin Majalisa gaba ɗaya domin kowane ɗan majalisa ya yi nazari.

Dasuki ya yi gargadin cewa aiwatar da dokoki daban da waɗanda Majalisar ta amince da su su kasance a gaban ’yan Najeriya zai zubar da mutuncin majalisa kuma saba wa kundin tsarin mulki ne.

“Mai girma shugaban majalisa, ina roƙo cewa dukkan takardun su zo gaban Kwamitin Majalisa gaba ɗaya. Dukkan ’yan majalisa su ga abin da ke cikin kwafin da aka fitar su kuma kwatanta da abinda suka amince da shi a zauren majalisa, domin mu yi gyaran da ya dace, Wannan yin karan tsaye ne ga kundin tsarin mulki.

“Wannan karya dokokinmu ne, kuma bai kamata wannan majalisa mai alfarma ta ɗauki wannan abu da wasa ba. Na gode shugaban majalisa,” in ji shi.

Kakakin Majalisa Abbas Tajudeen, wanda ya jagoranci zaman, ya ce ya lura da batun da Dasuki ya gabatar, kuma ya tabbatar da cewa za a ɗauki mataki kan lamarin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *