Zargin ɓatanci: Kwamitin Shura na Kano ya fara sauraron koke-koke kan Malam Triumph

[ad_1]



Gwamnatin Jihar Kano ta miƙa ƙorafe-ƙorafen da aka yi a kan Malam Shu’aibu Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph, ga Kwamitin Shura na Jihar don ɗaukar matakin da ya dace.

Sakataren Gwamnatin Jihar ne, ya tura ƙorafe-ƙorafen a ranar Juma’a, inda kwamitin ya fara zama domin sauraronsu.

A cewar kwamitin, za a gayyaci masu ƙorafi da Malam Triump domin su gabatar da hujjoji.

Masu ƙorafi za su fayyace abubuwan da suke tuhumar malamin, yayin da shi kuma za a ba shi damar kare kansa.

Bayan haka kwamitin zai tattauna bisa ƙa’idojin shari’ar Musulunci.

Sakataren kwamitin, Shehu Wada Sagagi, ya shaida wa manema labarai cewa an yi hakan ne domin tabbatar da adalci.

“Bayan mun saurari ɓangarorin biyu, kwamitin zai tattauna sannan ya bai wa gwamnatin jiha shawarwari,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin masu ƙorafin sun yi barazanar kai ƙara kotu, amma ya roƙe su da su bari kwamitin Shura ya yi aikinsa.

“Muna kira ga jama’a da su ci gaba da zama cikin lumana. Kano na daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Arewa maso Yamma, kuma wajibi ne mu kiyaye wannan zaman lafiya don ci gaban tattalin arziƙi da zamantakewa,” in ji shi.

Sagagi ya ce kwamitin ya ƙunshi manyan malamai da suka ƙware a fannin shari’ar Musulunci, kuma za su bai wa gwamnati shawarar da ta dace.

Aminiya ta ruwaito cewa, cikin tuhumar da ake yi wa Malam Triump har da kalaman ɓatanci a kan Fiyayyen Hallita, Annabi Muhammad (SAW), yin tambaya kan haihuwarsa, da kuma cewa iyayensa suna cikin wuta.

Har ila yau, masu ƙorafin sun ce yana yin wasu maganganu da suka ɗauke su a matsayin raini.

Kwamitin ya yaba wa gwamnatin jihar na bai ba shi damar warware matsalar ta hanyar tsarin Musulunci, maimakon a bari ya haddasa tashin hankali a cikin jama’a.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *