Gobarar kasuwar katakon Gombe ta lalata dukiyar biliyan 1.1 – ‘Yan kasuwa

[ad_1]



Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwar Katako ta Jihar Gombe, Malam Mohammed Ahmaduya ce gjinir da ta tashi sau biyu cikin wata a kasuwar katako ta jihar ta lalata dukiya da darajarta ta kai kimanin naira biliyan 1.1.

Ya ce lamarin ya jefa daruruwan ’yan kasuwa cikin mawuyacin hali.

A ranar Litinin ce wata sabuwar gobarar ta auku da daren Litinin a kasuwar, inda aka yi asarar kayayyaki da darajarsu ta haura naira miliyan 600 bayan da wuta ta kone shaguna da dama.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin ziyarar jaje da Mataimakin Gwamnan Jihar, Manasseh Daniel Jatau, ya kai wa ’yan kasuwar da abin ya shafa.

A cewarsa, gobarar ta tashi ne da misalin karfe 7:30 na dare, inda ta lalata shaguna fiye da 60 da ke dauke da katako da sauran kayan gini.

“A kalla kayayyaki da darajarsu ta kai naira miliyan 600 ne suka kone,” in ji shi, yana mai rokon gwamnatocin jiha da ta tarayya da su kai musu daukin gaggawa domin rage radadin asarar da suka yi.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Mataimakin Gwamna Jatau ya ce gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar hukumomin da abin ya shafa za su gudanar da cikakken bincike domin su tantance barnar domin samar da tallafin gaggawa ga wadanda abin ya shafa.

Ya kuma bukaci ’yan kasuwar da su yi nazari kan yawaitar tashin gobara a kasuwar, yana tunatar da cewa wani bangare na kasuwar ya fuskanci irin wannan iftila’i kimanin makonni uku da suka gabata.

Mataimakin gwamnan ya kuma shawarci ’yan kasuwar da su kara taka-tsantsan wajen amfani da wutar lantarki, tare da gode wa Allah da ba a rasa rai ba.

Ya jaddada cewa gwamnatin Gwamna Inuwa Yahaya na ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

A nasa bangaren, Shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA), Alhaji Abdullahi Haruna Abdullahi, ya ce ana ci gaba da aikin tantance barnar domin daukar matakan gaggawa.

Ya ce gobarar, kamar wasu da dama da suka rika faruwa a jihar, ana zargin matsalar lantarki ce ta haddasa ta.

A baya, a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2025, wata mummunar gobara ta lalata dukiya da darajarta ta haura naira miliyan 500 a Kasuwar Tsofaffin Karafa da Katako a Gombe.

Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwar Tsofaffin Karafa da Masu Dillancin Karafa, Abdullahi A.A. Laja, ya ce gobarar ta tashi ne cikin dare, ta kuma ci gaba har zuwa karfe 4:00 na asuba, inda ta kone shaguna sama da 30, dukkansu mallakinsa.

Laja ya dora girman barnar da aka yi kan jinkirin kai dauki daga bangaren jami’an kashe gobara, yana mai cewa fiye da ’yan kasuwa 100 ne wannan masifa ta shafa.

Da aka hada gobarar biyu, sama da shaguna 90 ne suka lalace, tare da rugujewar hanyoyin samun abin dogaro ga daruruwan iyalai cikin wata guda.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *