Gwamnan Kano Na Shirin Komawa APC, Kwankwaso Ya Ja Tunga


Wasu rahota da jaridar Politics Digest suka ruwaito sun nuna cewa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kammala shirye-shiryen ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC gabanin zaɓen 2027. Majiyoyi sun shaida cewa gwamnan ya kammala tattaunawa da manyan abokan siyasa, kuma ana sa ran zai sanar da matsayinsa nan da kowane lokaci.

Bincike ya nuna cewa gwamnan ya daɗe yana matsa wa ubangidansa na siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ya bi sahunsa zuwa APC, amma Kwankwaso ya ƙi amincewa, yana mai jaddada cewa zai ci gaba da zama a NNPP. Duk da ƙoƙarin da aka yi jan shi APC, amma gwamnan bai samu goyon bayan Kwankwason ba.

  • Sarki Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Bayan Shafe kwana 25 A Hannun Masu Garkuwa A Kwara
  • Nijeriya Ta Tabbatar Da Kai Harin Amurka Kan Ƴan Ta’adda A Sokoto

Wata majiya daga Majalisar Dokokin Jihar ta ce gwamnan ya gana da wasu ‘yan majalisa tare da bayyana musu shirinsa na sauya jam’iyya, inda ake sa ran Kakakin Majalisar zai fitar da sanarwa na nuna goyon baya ga duk shawarar da gwamnan zai ɗauka.

Haka kuma, ana sa ran magoya bayan Kwankwaso za su fitar da wata sanarwa ta ƙarfafa biyayya ga jagoransu da jam’iyyar NNPP. Politics Digest ta bayyana cewa duk wani ƙaƙarin jin ta bakin kakakin gwamna da na Kwankwaso bai yi nasara ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *