Gwamnatin Tarayya ta tura jami’an tsaro 7,000 zuwa daji don yaƙi da ’yan bindiga

[ad_1]



Gwamnatin Tarayya ta tura sabbin jami’an tsaron gandun daji sama da 7,000 domin yaƙi da ’yan bindiga da sauran laifuka a faɗin Najeriya.

An ɗauki waɗannan jami’ai ne tare da horas da su a ƙarƙashin shirin ‘Ƙaddamarwar Shugabancin Gandun Daji’wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar a watan Mayun 2025.

Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Kan Harkokin Tsaro (ONSA) ne, ke kula da shirin.

A cewar wata sanarwa da Rabiu Ibrahim, mai taimaka wa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, ya fitar a ranar Asabar, jami’an sun kammala ɗaukar horo mai tsanani na tsawon watanni uku.

An gudanar da bikin kammala ba su horo a ranar Asabar, 27 ga watan Disamba, 2025, a jihohi bakwai da suka haɗa da Borno, Sakkwato, Yobe, Adamawa, Neja, Kwara da Kebbi.

Da yake jawabi a wajen bikin, Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkar Tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce jami’an tsaron gandun dajin za su taimaka wajen dawo da ikon gwamnati da kuma kare al’ummomin da ke fama da matsalar tsaro.

Ya ce jami’an za su kasance masu kai ɗauki da kare al’umma, da kuma masu tattara bayanan sirri tare da taimaka wa sauran hukumomin tsaro a yankunan da ’yan ta’adda suka mamaye.

Ribadu, ya bayyana cewa horon ya haɗa da kare muhalli da kuma barazanar tsaro.

An horas da jami’an kan ƙarfin jiki, sintiri, tsallake shingaye, fuskantar kwanton-ɓauna, ceto mutane, da sauran ayyukan tsaro a dazuka.

Ya ƙara da cewa za a fara tura jami’an aiki nan take, ba tare da ɓata lokaci ba.

Za su fara karɓar lbashi da alawus-alawus nan da nan, kuma duk wanda ya kammala horon zai wuce kai-tsaye wajen aikinsa.

Daga cikin duk waɗanda suka samu horon, kashi 98.2 sun kammala shi cikin nasara.

An sallami mutum 81 saboda rashin ladabi da karya dokoki, yayin da mutane biyu suka rasu sakamakon matsalolin rashin lafiya.

Gwamnati ta ce ana sa ran jami’an da suka kammala horon za su yi amfani da sanin wurare da kuma amincewar al’umma wajen yaƙi da ’yan bindiga, garkuwa da mutane, da kuma haramtattun ayyuka a dazuka.

Shirin jami’an tsaron gandun daji haɗin gwiwa ne tsakanin hukumomi da dama, ciki har da DSS, Hukumar Kula da Gandun Daji ta Ƙasa, Hedikwatar Tsaro, Sojojin Ƙasa da Ruwa, ’Yan Sanda, da Hukumar NSCDC.

Ribadu ya jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na tabbatar da tsaro, inda ya ce za a faɗaɗa shirin zuwa dukkanin jihohin Najeriya domin ƙara samar da zaman lafiya da tsaro.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *