Sojoji sun ceto tsohon Kanar da aka sace a Filato
Sojojin Runduna Operation Enduring Peace sun ceto wani tsohon Kanar ɗin soja, Ajanaku mai ritaya, daga hannun ’yan bindiga a yankin Rafiki da ke Ƙaramar Hukumar Bassa a Jihar Filato.
Mai riƙon muƙamin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar, Laftanar-Kanar Aliyu Danja, ya tabbatar da nasarar ceton tsohon jami’in soja.
“Ina tabbatar muku cewa dakardunmu sun ceto tsohon jami’in soja a daren jiya. Yanzu haka an kai shi cibiyar lafiyarmu domin a duba lafiyarsa,” in ji Danja.
Majiyoyi daga Bassa sun bayyana cewa ’yan bindiga sun shiga gidan Kanar Ajanaku da ke gaban Cocin Salvation Army a kan titin Rukuba, inda suka yi awon gaba da shi da misalin ƙarfe 12:45 na dare a ranar Litinin.