Amurka da Isra’ila sun ƙaddamar da sabbin hare-hare a Iran

[ad_1]



Ƙasar Isra’ila ta sanar da ƙaddamar da wani sabon hari na gargaɗi kan Iran a ranar Asabar, kamar yadda Ministan Tsaron ƙasar, Israel Katz, ya bayyana.

A cikin wata sanarwa, ma’aikatar tsaron Isra’ila ta ce ta kai harin ne a matsayin “hari na rigakafi” domin kawar da wata babbar barazana, inda aka ayyana dokar ta-ɓaci ta musamman a faɗin ƙasar.

Hakan ya biyo bayan ƙarar ƙararrawar gargaɗi a Jerusalem, tare da saƙonnin gargaɗi da aka tura wa jama’a ta wayar salula game da abin da aka kira “mummunar barazana”.

Rahotanni daga Iran sun ce an ji ƙarar fashewar bama-bamai da dama a babban birnin ƙasar, Tehran, a ranar Asabar.

Wani jami’in Amurka ya shaida wa Al Jazeera cewa hare-haren da aka kai an yi su ne ta hanyar haɗin gwiwar sojojin Isra’ila da Amurka.

Rahoton ya ce Amurka ta jibge manyan jiragen yaƙi da jiragen ruwan soji a yankin, domin matsa wa Iran lamba ta amince da yarjejeniya kan shirinta na makamashin nukiliya.

Sai dai har zuwa yanzu, ba a tabbatar da takamaiman wuraren da aka kai wa hare-haren ba, kuma hukumomi ba su fitar da bayanan asarar rayuka ko raunuka ba.

Wasu rahotanni sun nuna cewa ɗaya daga cikin hare-haren ya shafi wani yanki kusa da ofisoshin Jagoran Ƙoli na Addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

A cewar wata majiya da Reuters ta ambata, Ayatollah Khamenei ba ya cikin Tehran a halin yanzu, inda aka ce an sauya masa matsuguni zuwa wani wuri mai tsaro.

Ministan Sufuri, Miri Regev, ta bayar da umarnin rufe sararin samaniyar ƙasar baki ɗaya ga jiragen farar hula, a wani yunƙuri na ɗaukar mataki a sakamakon sabon yanayin tsaron da ya taso.

Ita ma Iraƙi ta sanar da rufe sararin samaniyarta, bayan Isra’ila ta tabbatar da kai hare-hare kan Iran, kamar yadda kafafen yaɗa labaran gwamnati suka ruwaito.

Hukumar labaran Iraƙi (INA) ta rawaito cewa ma’aikatar sufuri ta ƙasar ta fitar da sanarwar rufe sararin samaniyar Iraƙi gaba ɗaya, a wani mataki na kariya sakamakon sabon yanayin tsaro da ya taso a yankin.

An ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da tsaron zirga-zirgar jiragen sama, yayin da tashin hankali ke ƙara ƙamari tsakanin Isra’ila da Iran.

Har yanzu dai ana ci gaba da sa-ido kan lamarin, yayin da ƙasashen duniya ke nuna damuwa kan yiwuwar faɗaɗar rikicin da ke ƙara ƙamari tsakanin Isra’ila da Iran.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *