Tinubu ya yaba wa bajintar Super Eagles a Gasar AFCON
[ad_1]
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya yaba wa tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta Super Eagles kan kaiwa wasan kusa da ƙarshe a Gasar Kofin Afirka da ake bugawa a ƙasar Moroko.
Najeriya ta samu wannan nasara ce bayan da ta doke Aljeriya da ci 2-0 a birnin Marrakech, lamarin da ya bai wa tawagar damar tsallakawa zuwa matakin kusa da ƙarshe.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X jim kaɗan bayan kammala wasan, Shugaba Tinubu ya jinjina wa ƙoƙari da jajircewar ’yan wasan tawagar ƙasar.
“Lallai wannan bajinta da kuka yi namijin ƙoƙari ne abin burgewa. Ku ci gaba da jajircewa, domin dukan ’yan Najeriya na goyon bayanku,” in ji Tinubu.
A mako mai zuwa ne tawagar Najeriya za ta fafata da Moroko, mai masaukin baƙi, a wasan kusa da ƙarshe na gasar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link