Kafa Kamfanin Sarrafa Gwal A Legas: Ƙungiyar Dattawan Arewa Ta Ƙalubalanci Tinubu
[ad_1]
Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta zargi gwamnatin tarayya da gina kamfanin wanki da sarrafa gwal a Jihar Legas.
Farfesa Abubakar Jika Jiddere, mai magana da yawun ƙungiyar, ya sanya wa wata buɗaɗɗiyar wasiƙa hannu, wadda ƙungiyar ta wallafa, ta kuma miƙa wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mambobin majalisar zartarwa ta tarayya.
Wasiƙar mai ɗauke da kwanan wata na 18 ga watan Junairu 2026, mai suna “Buɗaɗɗiyar wasiƙa ga gwamnatin tarayyar Nijeriya, kan wurin da za a kafa kamfanin wanki da sarrafa gwal na ƙasa, akwai buƙatar samar da daidaito, domin kauce wa rikici”.
A ranar Talata 13 ga wata, ministan ma’adinai na ƙasar, Dele Alake, yayin wata ganawa da ministan masana’antu da albarkatun ma’adinai na ƙasar Saudiyya, Ibrahim Al-Khorayef, wanda aka gudanar gabanin taron ma’adinai na a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya, ya sanar da fara aikin a wata cibiyar tace gwala-gwalai mai tsafta a Legas.
- Gwamnonin Arewa Sun Yi Allah-Wadai Da Harin Kasuwar Neja
- Majalisa Ta Yaba Wa ‘Yansanda Kan Gaggawar Kama Waɗanda Ake Zargi Da Kisan Gilla A Kano
Ministan, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Segun Tomori, ya fitar, ya kuma ce; ana ci gaba da samar da ƙarin kamfanonin sarrafa gwal ɗin guda uku a sassan faɗin wannan ƙasa, sannan kuma kamfanin sarrafa ‘lithium’ na dala miliyan 600 da ke Jihar Nasarawa, a shirye yake ya fara aiki.
Ƙungiyar Dattawan Arewan, a cikin wasiƙarta, ta ce; yanke shawarar kafa kamfanin na sarrafa gwal a Legas, lallai akwai alamun tambaya a kai, duba da yadda aka gudanar da shi.
Wasiƙar ta ƙara da cewa, “Masu Girma, Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), sun fitar da wannan buɗaɗɗiyar wasiƙa, ba da zummar zanga-zanga ko bore ba, illa a matsayin duba kan tsarin mulki, tattalin arziƙi da kuma shiga tsakani na siyasa da gwamnatin tarayya ta yanke na kafa kamfanin sarrafa gwal a Jihar Legas, duk kuwa da cewa; waɗannan ma’adanai na zube ne a yankin Arewacin Nijeriya.
“Sashe na 14 (3) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya, 1999 (kamar yadda aka gyara), ya tanadi ƙa’idar rabon kaso na tarayya, wanda ke ba da umarni cewa; tsari da gudanar da harkokin gwamnati, dole ne su nuna bambancin Nijeriya da kuma hana mamaye ko ware kowane rukuni ko yanki.
“Bugu da ƙari, sashe na 16 (1) (b), ya wajabta wa jiha ta kula da tattalin arziƙin ƙasa ta yadda za ta tabbatar da ‘mafi girman walwala, ‘yanci da jin daɗin kowane ɗan ƙasa, bisa tushen adalci na zamantakewa da daidaiton matsayi da bayar da dama.”
Taron ya ce, manufar da ke fitar da arziƙin ma’adinai daga yanki guda, yayin da ake gano ƙarin darajar, ayyukan masana’antu da tarin jari a wasu wurare, ya sava wa wannan umarni.
Ƙungiyar ta jaddada cewa, hana yankunan da ke samar da wannan arziƙi na gwal amfana tare da samar da masana’antu da ci gaba, na nuni da cewa; an ajiye ƙa’idar nan ta bai wa yankin da ke tattare da arziƙi wani kaso daga cikin kashin da kundin tsarin mulki ya ba shi.
“Arewacin Nijeriya, musamman Jihohin Zamfara, Kebbi, Neja, Kaduna, Katsina da sauran yankunan da ke maƙwabtaka da su, gurvacewar muhalli, tavarvarewar al’umma, rashin tsaro da kuma hanyoyin da suka shafi haƙar ma’adanai, ba bisa ƙa’ida ba da zalunci, sun mamaye su.”
Ƙungiyar ta ce, dole ne gwamnatin tarayya ta fuskanci illar siyasantar da wannan ƙuduri, inda ta bayyana cewa; Nijeriya na fama da matsalar rashin daidaito, inda dukiyoyin gwamnatin tarayya da tarin masana’antu da ƙarfin tattalin arziƙi, suka taru a Legas da kewayenta.
A saƙonta kai tsaye zuwa ga jiga-jigan Arewa, shugabannin siyasa da masu ruwa da tsaki, ƙungiyar NEF ta ce; tarihi ba zai tava girmama waɗanda suka ga rashin adalci a fili, kuma suka zavi yin shiru fiye da jajircewa ba, sannan ta bayyana matakin kafa kamfanin gwal a Nijeriya cikin Jihar Legas, bayan haƙo zinaren daga Arewacin ƙasar a matsayin wani babban kuskure na siyasa, wanda a cewar tata, wani shiri ne na lalata tattalin arziƙi.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa, tarihi ba zai manta da shugabannin da suka yi watsi ko yin shuru, domin neman biyan buƙata ko samun wani tasiri ba, tana mai jaddada cewa; “A halin yanzu, ana rubuta waɗannan bayanai, ba za kuma a yi kuskuren uzurin fahimtar yin shiru ba, za a tuna da su a nan gaba a matsayin cin amana.”
Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Iƙirarin Ƙungiyar NEF Kan Kafa Kamfanin Sarrafa Gwal A Legas
Gwamnatin tarayya, ta yi watsi da iƙirarin da Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta yi, na zargin karya ƙa’idar ɗa’a ta tarayya a wajen kafa kamfanin sarrafa gwal a Jihar Legas.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga Ministan Ma’adanai na Ƙasa, Segun Tomori, ya bayyana zargin ƙungiyar ta NEF, a matsayin vatanci kan kalaman da ministan ma’adinan, Dokta Dele Alake ya yi, kan sauye-sauyen da ake yi da kuma zuba hannun jari a vangaren ma’adinai.
“Babu inda ministan ma’adinan ya sanar da cewa, gwamnatin tarayya za ta kafa kamfanin gwal a Legas ko a wani wuri daban,” in ji Tomori. “Dr. Dele Alake ya bayyana ƙarara cewa, sauran kamfanonin sarrafa gwal ɗin, na nan ana kan aikin gina su a sassan faɗin ƙasar, sannan kuma dukkaninsu na kamfanoni masu zaman kansu ne.”
Tomori ya fayyace cewa, kamfanin sarrafa gwal ɗin da ƙungiyar ta NEF ta ambata, wani shiri ne mai zaman kansa na kamfanin Kian Smith, wanda aka kafa don bunƙasa masana’antar gwal na cikin gida a Nijeriya.
Ya nanata cewa, gwamnatin tarayya ba ta tilasta wa ƴan kasuwa wuraren da ya kamata su gudanar da kasuwancinsu ba, yana mai cewa; irin waɗannan shawarwari, na da nasaba da buƙatun wasu kamfanoni da na kasuwanci.
“Gwamnatin tarayya, ba ta mallaki ko kafa kamfanin sarrafa gwal a Legas ko a wani wuri a faɗin ƙasar nan ba,” in ji shi, inda ya buƙaci jama’a da su bambance ayyukan gwamnati da zuba jari na kamfanoni masu zaman kansu.
A cewarsa, ma’aikatar ta ci gaba da jajircewa wajen samar da yanayi mai kyau na bunƙasa ma’adanai masu inganci a dukkan sassan wannan ƙasa.
Gwamnatin Zamfara Ta Yi Zargin Nuna Rashin Adalci A Kafa Kamfanin A Legas
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Zamfara, Mahmud Muhammad Dant-awasa, a wata tattaunawa da ya yi da ɗaya daga cikin ƴan jarida a jiya, ya yi zargin cewa; yanke shawarar kafa kamfanin sarrafa gwal a Legas, rashin adalci ne.
“Don haka, idan har gwamnatin tarayya ta na da gaskiya a kan wannan batu, ya kamata a samar da kamfanin a Jihar Zamfara, ba Legas ba. Idan batun ma’adanai na zinari ko gwal, babu wata jiha a duk faɗin tarayya da za ta iya yin takara da Zamfara.
“Duk da cewa, muna fuskantar ƙalubale na tsaro, hakan bai kamata ya zama hujjar yin watsi da jihar daga abin da ta dace ba. Domin kuwa, gwamnatin tarayya ta fi ƙarfin kowace irin ƙungiya ta ‘yan ta’adda ƙarfi.”
Shi ma da yake yin nasa tsokacin, kwamishinan kasuwanci da masana’antu na Jihar Zamfara, Abdulrahman Tumbido ya ce; jihar ta haɗa kai tare da goyon bayan Ƙungiyar Dattawan Arewa, tana mai kira ga gwamnatin tarayya da ta duba matakin da ta ɗauka.
“Kungiyar Dattawan Arewar ta faɗi gaskiya, kuma idan gwamnatin tarayya ta yarda ta yi adalci a kan hukuncin da ta yanke, ya kamata a mayar da kamfanin sarrafa gwal ɗin zuwa Jihar Zamfara, har jihohin Kebbi, Neja da Kaduna ba za su iya yin takara da Zamfara ba, idan ana batun abin da ya shafi arziƙin zinari ko gwal.
[ad_2]
Source link