Kotun Ƙoli ta wanke Al-Mustapha daga zargin kisan Kudirat Abiola
[ad_1]
Kotun Kolin Najeriya ta kori shari’ar da ake yi wa Manjo Hamza Al-Mustapha, tsohon Babban Jami’in Tsaron na marigayi Shugaban Soja, Janar Sani Abacha, kan kisan ’yar siyasa, Alhaja Kudirat Abiola.
Kudirat Abiola ita ce matar marigayi dan kasuwa kuma dan siyasa, Cif MKO Abiola, wanda ake ganin shi ya lashe zaben shugaban kasa na 12 ga Yuni, 1993, da tsohon Shugaban Kasa Ibrahim Babangida ya soke.
An kashe Kudirat Abiola a Legas a lokacin rikicin da ya biyo bayan soke zaben, a yayin da take ci gaba da fafutukar ganin sojoji sun janye sokewar.
Kwamitin alkalan kotun biyar karkashin jagorancin Mai Shari’a Uwani Abba-Aji a ranar Alhamis ya kori tuhumar da Gwamnatin Jihar Legas ke yi wa tsohon sojan.
A zaman kotun, Gwamnatin Jihar Legas ta kasa sake bude shari’ar, kuma ba ta gabatar da lauya ko wata takarda ba tun daga lokacin da aka ba ta damar yin hakan a 2014.
Lokacin da aka kira shari’ar, lauyan Al-Mustapha, Paul Daudu (SAN), ya shaida wa kotu cewa Legas ba ta dauki wani mataki ba don aiwatar da umarnin da aka ba ta a 2014 na sake bude shari’ar.
Babban lauyan ya shaida wa kotun cewa a 2014, lokacin da aka ba da umarnin sake bude shari’ar, an ba Legas wa’adin kwanaki 30 don gabatar da sanarwar daukaka kara.
Sai dai ya ce bayan shekaru da dama, jihar ba ta yi komai ba don bin umarnin.
Ya ce mai daukaka kara ya yi watsi da shari’ar, don haka ya kamata a kori shari’ar baki daya.
Mai Shari’a Uwani Abba-Aji, wadda ta jagoranci zaman, ta tambayi ko Legas ta samu sanarwar sauraron shari’a; inda magatakardar kotun ya tabbatar da hakan.
A yayin yanke hukunci, kwamitin ya yanke cewa Legas ba ta da sha’awa ci gaba da shari’ar, don haka ta yi watsi da ita.
Mai Shari’a Abba-Aji ta kuma ce shekaru tara sun isa mai daukaka kara ya gabatar da sanarwar daukaka kara da takaitaccen bayanin daukaka kara a kan shari’ar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link