Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

[ad_1]


An gudanar da tarukan bita a jiya Jumma’a a duka bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan domin nuna muhimmancin taron nan mai tarihi da ya gudana tsakanin shugabannin bangarorin biyu a shekarar 2015.

An gudanar da taron ne tsakanin Xi Jinping da Ma Ying-jeou a Singapore a ranar 7 ga Nuwamba, shekarar 2015, wanda ya kasance na farko tsakanin shugabannin bangarorin biyu na mashigin tekun Taiwan tun bayan shekarar 1949.

Da take jawabi a wani taron bita da aka gudanar a jiya Jumma’a a Taipei don tunawa da cika shekaru 10 da taron na shekarar 2015 mai tarihi, Cheng Li-wun, shugabar jam’iyyar Kuomintang (KMT) ta kasar Sin, ta ce gaskiyar lamari ta tabbatar da cewa yarjejeniyar 1992 da aka cimma za ta iya rage fargaba tsakanin bangarori biyu na mashigin tekun da kuma saukake musaya da cudanya cikin lumana, tana mai ba da misali da yawan musaya da cudanyar da aka yi tsakanin bangarorin biyu a tsakanin 2008 da 2016 bisa yarjejeniyar.

Kazalika, duk dai a jiya Jumma’ar, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da taron, Chen Binhua, mai magana da yawun Ofishin Harkokin Taiwan na Majalisar Gudanarwar Kasar Sin ya ce taron wanda ya gudana shekaru goma da suka gabata ya karfafa muhimmiyar rawar da Yarjejeniyar 1992 ta taka a matsayin ginshikin siyasa ta bunkasa zaman lumana a dangantakar bangarori biyu na mashigin tekun, kana matukar an ci gaba da amincewa da Yarjejeniyar 1992 kuma aka nuna adawa da batun “‘yancin kai na Taiwan”, to dangantakar bangarorin biyu za ta iya bunkasa cikin lumana kuma za a iya kara inganta muradun ‘yan kasa da ke bangarorin biyu na mashigin tekun. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *