’Yan sanda sun kama matashin da ya yi garkuwa da kansa a Ondo

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ondo, ta cafke wani matashi mai suna Azeez Bello, mai shekaru 29, wanda ya kitsa garkuwa da kansa domin karɓar kuɗin fansa Naira dubu 500 daga hannun iyayensa.

Kakakin rundunar, Ayanlade Olushola, ya bayyana cewa Bello, ɗan asalin garin Ipele da ke Ƙaramar Hukumar Owo, ya yi haka ne bayan mahaifinsa ya ƙi ba shi kuɗin da ya nema don yin kasuwanci.

A ranar 11 ga watan Agusta, Bello ya shaida wa iyayensa cewa zai tafi Ibadan, amma maimakon haka ya ɓoye kansa a Ipele.

Daga nan ya riƙa kiran iyayensa da abokansa yana cewa an yi garkuwa da shi kuma sai an biya kuɗin fansa kafin a sake shi.

Bello, ya ba da lambar asusun banki domin a saka kuɗin fansar.

Amma kafin a biya kuɗi , iyayensa suka sanar da jami’an ’yan sanda.

Jami’an tsaro sun bi diddgin lambar waya, inda suka gano wajen da ya ɓuya, sannan suka cafke shi.

Olushola, ya ce Bello ya amsa laifinsa, kuma idan aka kammala bincike, za a gurfanar da shi a kotu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *