NDLEA Ta Cafke Mai Safarar Kwayoyi Da Ta Yi Cikin Bogi

[ad_1]

Jami’an NDLEA sun kama wata ’yar kasuwa mai shekara 35, Rabi Muhammad, da ake zargi da safarar kwayoyi ta hanyar yin cikin bogi domin ɓoye haramtattun kwayoyi. Daraktan Yaɗa Labarai na hukumar, Femi Babafemi, ya ce an tare ta ne a kan iyakar Seme yayin da take ƙoƙarin wucewa zuwa Cotonou, Jamhuriyar Benin.

A cewarsa, jami’ai sun fara zargin ta ne bayan sun lura da kumburin cikinta. Amma binciken jiki ya gano cewa cikin na bogi ne, inda ta ɓoye kwayoyin tramadol 3,200 a cikin wata kwarya mai launin ruwan hoda da ta ɗaure a cikinta domin kai su sayarwa a Cotonou.

  • NDLEA Ta Cafke Wani Dan Kasuwa Mai Shirin Tafiya China A Filin Jirgin Saman Kano Dauke Da Muggan Kwayoyi
  • NDLEA Ta Yi Alkawarin Kwace Kadarorin Da Ke Ba Da Mafaka Ga Dillalan Kayoyi

A wani sumame daban, jami’an NDLEA a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano International Airport sun kama wani ɗan ƙasar Ivory Coast, Michael Gohouri, mai shekara 41, yayin da yake shirin tafiya Milan ta jirgin Ethiopian Airlines ta Addis Ababa. Binciken na’urar duba ciki ya tabbatar da ya haɗiye kwayoyi, inda daga bisani ya fitar da kunshi 82 na hodar iblis mai nauyin kilo 1.49. An ce za a biya shi Euro 5,000 bayan ya kai kayan Milan.

Haka kuma, NDLEA ta cafke Shugaba kuma Babban Daraktan kamfanin Trans Fortress Global Resources, Kolapo Oladapo Raji, a gidansa da ke Ikate, Lekki, Lagos. An ce ya kasance cikin jerin waɗanda ake sa ido a kansu tun 2025, inda aka kwato buhuna huɗu dauke da tabar wiwi nau’in “Canadian Loud” mai nauyin kilo 89.20, kuma ana zargin ya amsa cewa yana ɗaukar nauyin safarar kwayoyi kafin kafa nasa tsarin rarrabawa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *