Hisbah Ta Kano Ta Kama Matasa 583 Bisa Zargin Rashin Ɗa’a A Lokacin Sallah


Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama akalla matasa 583 bisa zargin aikata abubuwan da suka sabawa tarbiyya a lokacin bukukuwan Eid-el-Fitr da aka kammala kwanan nan a jihar.
An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Mataimakin Babban Kwamandan hukumar, Mujahid Aminuddeen, ya fitar a ranar Talata, wacce aka rabawa manema labarai.
“Yayin Sallah, jami’anmu sun samu nasarar kama matasa maza da mata fiye da 583, bisa aikata laifuka daban-daban na rashin da’a.
  • An Gurfanar Da El-Rufai A Kotun Kaduna, An Hana ‘Yan Jarida Shiga
  • Kama El-Rufai Tsagwaron Siyasa Ce Kuma Babu Adalci — Obi
“Kamar yadda kuka sani, mun tura jami’ai kimanin 9,500 a fadin jihar domin dakile irin wadannan halaye, kuma hakan ya haifar da sakamako mai kyau,” in ji shi.
Aminuddeen ya bayyana cewa an kama direbobin adaidaita sahu 275 saboda yin kitso da kuma sanya salon gashi da aka dauka bai dace ba kuma ya sabawa koyarwar addinin Musulunci.
A cewar hukumar, wadannan kamen sun kasance wani bangare ne na yakin da take yi da nufin tsaftace al’umma a jihar.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *