MTN zai rufe ofisoshi 101 a Kano, Borno da Adamawa saboda gyare-gyare
Kamfanin sadarwa na MTN ya sanar da shirin gudanar da aikin gyare-gyare a cibiyoyin sadarwa a ranar Asabar, 25 ga watan Oktoba mai zuwa.
Ana sa ran aikin zai kawo tsaiko na ɗan lokaci ga sadarwa a wasu sassan jihohin Adamawa, Borno da Kano.
MTN ya ce aikin zai ɗauki tsawon sa’o’i biyu, daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa 8:00 na safe, inda zai shafi ofisoshi 101 na cibiyar sadarwa a cikin ƙananan hukumomi 15 a jihohi ukun.
Kamfanin ya ce aikin yana cikin wani dogon shiri na inganta ayyuka da ƙarfafa tsarin sadarwa a Arewacin Najeriya.
Aikin zai haɗa da sauya wayoyin sadarwa na cable a wani ɓangare da aka matsar daga AFCOT zuwa kauyen Bawo, inda za a maye gurbin ɓangarorin wayoyin da suka lalace.
Yankunan da gyaran zani sda
MTN ya ce yankunan da gyaran zai shafa sun haɗa da Karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano; Girei, Song, Mubi North, Hong, Gombi, Fufore, Mubi South, Madagali, Michika, Maiha, Chibok da Yola ta Arewa a jihar Adamawa; da kuma Askira/Uba da Shani a jihar Borno.
Kamfanin ya ce sabis din 2G da 3G da 4G ba za su yi aiki ba a lokacin aikin.
MTN ta ce wannan mataki yana gina kan aikin dawo da cibiyar sadarwa da aka gudanar a watan Agusta 2025 a kan hanyar igiyar sadarwa ta AFCOT–Bawo.
Kamfanin ya ce abokan huldarsa na iya fuskantar tsaiko na ɗan lokaci, kuma ya ba da hakuri kan duk wata matsala da hakan zai iya haifarwa.