Majalisa Ta Yaba Wa ‘Yansanda Kan Gaggawar Kama Waɗanda Ake Zargi Da Kisan Gilla A Kano
[ad_1]
A ranar Laraba ne Majalisar Dattawa, ta hannun Kwamitinta kan Harkokin ‘Yansanda, ta yaba wa Rundunar ‘Yansandan Nijeriya (NPF) kan yadda aka kama wadanda ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi wa wata mata da ‘ya’yanta shida a Jihar Kano cikin gaggawa.
Waɗanda ake zargin, Umar Auwalu da Waɗanda suka taimaka masa su biyu, sun kai hari gidan wata matar aure, Fatima Abubakar, a unguwar Chiranchi Dorayi, a karamar hukumar Gwale ta Jihar Kano a ranar Asabar da ta gabata, inda suka kashe ta da ‘ya’yanta shida.
- Tsaro: Gwamnatin Nijeriya Ta Ɗauki Rayukan Mutane Da Muhimmanci – Peter Obi
- ’Yan Bindiga Sun Sace Mutane Sama Da 20 A Katsina
A wani samame da ‘yansanda suka kai, sun kama Auwalu da sauran wadanda ake zargin su biyu a ƙasa da sa’o’i 20 bayan faruwar lamarin.
Da yake mayar da martani ga wannan lamari, shugaban kwamitin harkokin ‘yansanda na Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Malam-Madori, a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Laraba a Abuja, ya bayyana kama waɗanda ake zargin da gaggawa a matsayin wata alama a fili ta ƙwarewar aikin rundunar da ke ƙara samun karɓuwa, ta hanyar amfani da leken asiri.
“Saurin bin diddigin waɗanda ake zargin da kuma kama su akan lokaci ya nuna ƙwarewar aikin rundunar ‘yansandan Nijeriya,” in ji shi.
[ad_2]
Source link