Mutum Ɗaya Ya Rasu, Tsohon Mataimakin Gwamnan Katsina Ya Jikkata A Hatsarin Mota

[ad_1]

Wani mutum ya rasu yayin da wasu suka jikkata a hatsarin mota a Katsina. Hatsarin ya rutsa da wakilan APC daga Sabuwa kan hanyarsu ta zuwa taron yankin Arewa maso Yamma na jam’iyyar.

Rahotanni sun nuna cewa marigayin mai suna Dalhat Machika na cikin waɗanda suka mutu. Haka kuma tsohon mataimakin gwamna, Sirajo Umar Damari, ya ji rauni tare da shugaban APC na Sabuwa.

  • 2027: Cikin Ƴan APC Ya Ɗuri Ruwa Saboda Tasirin Makinde  – Ƙungiyar PDP
  • Gwamnatin Kano Ta Bai Wa Masu Son Yin Takara Wa’adin Yin Murabus Daga Muƙamansu

DailyTrust ta rawaito cewa, mai magana da yawun gwamnan jihar, Ibrahim Kaula, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce ana kula da waɗanda suka jikkata a asibitin Yusuf Dantsoho Memorial da ke Kaduna.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya ziyarci asibitin bayan kammala taron APC. Ya jajanta wa iyalan mamacin tare da yi wa waɗanda suka jikkata addu’ar samun sauƙi.

Sanarwar ta ce gwamnan ya tabbatar da tallafin gwamnati ga waɗanda abin ya shafa. Ya kuma ziyarci asibitin tare da wasu manyan jami’an gwamnati domin duba halin da ake ciki.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *