Gwamnan Kano Ya Sauke Shehu Wada Sagagi Daga Muƙamin Kwamishina

[ad_1]

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauke Shehu Wada Sagagi daga muƙamin kwamishina. Sagagi ya kasance Kwamishinan Zuba Jari, Kasuwanci da Masana’antu.

Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta tabbatar da hakan. Ta ce an umurce shi da ya miƙa ragamar ma’aikatar nan take.

  • Eid-el-Fitr:Kwankwaso Ya Buƙaci Magoya Bayansa Su Ci Gaba Da Jajircewa Kan Kyawawan Manufa
  • Hukumar Shari’ah Ta Kare Zargin Da Amurka Ke Yi Wa Kwankwaso

Gwamnan ya nuna godiya ga irin gudunmawar da Sagagi ya bayar a lokacin aikinsa. Ya jaddada rawar da ya taka a fannonin siyasa, da addini da bunƙasa ƙanana da matsakaitan sana’o’i.

Ya kuma yi masa fatan alheri a matakai na gaba a rayuwarsa. Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da inganta ayyukan yi wa jama’ar jihar hidima. Sanarwar ta ce matakin na daga cikin gyaran tsarin gwamnati domin ci gaba mai ɗorewa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *