Sojoji sun kama babban mai safarar makamai ga ’yan ta’adda a Kuros Riba




Rundunar Sojin Najeriya karkashin runduna ta 245 da ke Kalaba, ta samu nasarar cafke wani shahararren mai safarar miyagun makamai ga ’yan ta’adda a yankin Abi na Jihar Kuros Riba.

Manjo Yemi Sokoya, Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar ta 13, ya ce an kama wanda ake zargi mai suna Ojo Friday, ɗan asalin ƙauyen Ochon a ƙaramar hukumar Obubra, mazaunin garin Abomege da ke Jihar Ebonyi.

A cewar Sokoya, jami’an sojin da ke sintiri bisa bayanan sirri sun yi dirar mikiya suka cafke wanda ake zargi tare da akwatunan harsasai da bindiga mai sarrafa kanta da yake sayarwa ’yan ta’adda.

Kwamandan rundunar, Birgediya Janar P.O. Alimikhena, ya ce wannan nasara ta nuna ƙwarewar jami’an sojin wajen gudanar da ayyukansu.

Ya kara da cewa, “Jami’anmu sun nuna hazaka da gogewa wajen kare martabar ƙasa da al’umma.”

A halin yanzu, wanda aka kama yana tsare a hannun sojoji, inda ake ci gaba da gudanar da bincike a kansa domin samun ƙarin haske kan safarar makaman da ake zarginsa da aikatawa.

Brigadiya Janar Alimikhena ya yi jinjina ga jami’an da suka gudanar da aikin, tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da yin aiki tuƙuru domin kare martabar ƙasa da tsaron al’umma.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *