Atiku Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan Uwa Da Ƴaƴanta Shida A Kano

[ad_1]

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da kisan wata mata da ƴaƴanta shida da aka yi a unguwar Dorayi Chiranchi, cikin birnin Kano, yana bayyana lamarin a matsayin abin takaici da ba za a amince da shi ba. A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Atiku ya ce ya kaɗu matuƙa da wannan mummunan kisa, tare da miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan da ma al’ummar yankin baki ɗaya.

Ina matuƙar jimami da kisan gilla da aka yi wa uwa da ƴaƴanta shida a Dorayi Chiranchi, a Kano. Wannan tashin hankalin da ba shi da dalili ga fararen hula ba za a taɓa yarda da shi ba. Zuciyata da addu’o’ina suna tare da iyalan da suka rasa ƴan uwansu da kuma al’ummar yankin,” in ji Atiku.

  • Ɗan Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar Ya Koma APC
  • AFCON 2025: Muhimman Abubuwa Da Ya Kamata Ku Sani Game da Wasan Karshe Tsakanin Senegal Da Morocco

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma nuna damuwa kan tasirin matakan tsaro da ake ɗauka, yana tambayar ko umarnin da ake bayarwa ga hukumomin tsaro na samun aiwatarwa yadda ya kamata.

Tun da farko, rundunar ƴansandan Jihar Kano ta tabbatar da cafke wasu mutane uku da ake zargi da hannu a kisan matar da ƴaƴanta shida. A cewar ƴansanda, an kama su ne bayan wani sumame da aka gudanar bisa bayanan sirri tsakanin daren ranar 17 da safiyar 18 ga Janairu, 2026. Lamarin ya ci gaba da jawo Allah-wadai daga shugabannin siyasa da ƙungiyoyin farar hula.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *