Gwamnatin Gombe da Rotary sun yi shirin rage mutuwar mata da yara
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Gombe tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Rotary International sun ƙaddamar da shirin aikin jinya domin rage mace-macen mata da yara a faɗin jihar.
Shirin da aka gudanar a Ƙananan hukumomi uku da suka haɗa: Gombe da Kaltungo da Yamaltu-Deba, inda aka yi wa jama’a gwaje-gwaje, jinya da wayar da kai a unguwannin Yelenguruza da Kagarawal.
Shugaban Rotary Reproductive, Maternal and Child Health a Nijeriya, Farfesa Emmanuel Adedolapo Lufadeju, ya bayyana cewa fiye da mutum 120 aka duba a unguwar Kagarawal kaɗai, inda aka samu kashi 70 cikin 100 sun kamu da zazzaɓin cizon sauro.
Ya ce, tun daga shekarar 2013 Rotary ke gudanar da irin wannan shiri a sassa daban-daban na ƙasar, kuma ya bayyana na Gombe a matsayin ta daban wanda aka gudanar a wurare biyu lokaci guda.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Habu Dahiru ya yaba wa Rotary bisa haɗin gwiwa tare da kira ga jama’a su riƙa cin moriyar asibitocin da gwamnati ta sabunta a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.
Ya shawarci mata masu juna biyu da su riƙa zuwa duba lafiya a asibiti, kana iyaye su tabbatar da yin allurar rigakafi ga ‘ya’yansu ’yan ƙasa da shekara biyar domin kare su daga mutuwa marar dalili.
Wasu daga cikin al’ummar da suka ci gajiyar shirin a Unguwar Kagarawal sun nuna farin ciki da godiya ga gwamnati da abokan haɗin gwiwa bisa kawo musu tallafin jinya a kusa da su.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link