An Gudanar Da Dandalin Kafofin Watsa Labarai Na Sin Da Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo A Birnin Kinshasa
[ad_1]
An gudanar da dandalin kafofin watsa labarai na Sin da janhuriyar dimokaradiyyar Congo a jiya Laraba a birnin Kinshasa, bisa taken “Zamanantarwar kasar Sin da turbar ciyar da janhuriyar dimokaradiyyar Congo gaba: Hada karfi wajen lalubo sabbin hanyoyin cimma gajiya tare, da hadin gwiwar cimma moriyar bai daya,” taron da ya hallara kimanin mutane 250, ciki har da ’yan siyasa, da wakilan kafofin watsa labarai, da jagororin ’yan kasuwa na kasashen biyu.
Cikin sakonsa ta kafar bidiyo yayin bude dandalin, shugaban kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, Fu Hua, ya ce a bana ake cika shekaru 70 da kafuwar dangantakar diflomasiyya tsakanin Sin da nahiyar Afirka, kana a banan ne ake bikin shekarar musaya tsakanin al’ummun Sin da na nahiyar Afirka.
Fu Hua, ya kara da cewa Xinhua zai dauki wannan dandali a matsayin dama ta aiki tare da takwarori na kafofin watsa labarai dake janhuriyar dimokaradiyyar Congo, wajen zurfafa aiwatar da kudurori da shugabannin kasashen biyu suka zayyana.
A nasa bangare kuwa, mataimakin firaministan janhuriyar dimokaradiyyar Congo, kana ministan ma’aikatar bunkasa tattalin arzikin kasar Daniel Mukoko Samba, cewa ya yi dadaddiyar alakar Sin da janhuriyar dimokaradiyyar Congo ta ci gaba da bunkasa, bisa hadin gwiwa da abotar da suke rayawa. Kazalika, hadin gwiwa tsakanin nahiyar Afirka da Sin ta samar da muhimmin tallafi na bunkasa ci gaban nahiyar Afirka. Har ila yau, Mukoko ya ce kafofin watsa labarai suna taka rawar gani wajen cike gibin tuntubar juna, da taimakawa wajen bunkasa fahimtar juna tsakanin al’ummun kasashen biyu, da zurfafa hadin gwiwar Sin da janhuriyar dimokaradiyyar Congo. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link