Dalilin da ya sa ban ɗaga hankalina ba lokacin da na rasa muƙamai — Sanusi II

[ad_1]



Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) kuma Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana dalilin da ya sa bai ɗaga hankalinsa ba bayan rasa manyan muƙamai biyu a rayuwarsa.

Sanusi II, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron lakcar azumi ta shekara-shekara ta Fola Adeola (Fola Adeola Annual Ramadan Lecture).

A wajen taron, ya yi magana kan muhimmancin haƙuri da kuma yadda dogaro da Allah Ya taimaka masa wajen shawo kan ƙalubalen da ya fuskanta.

Ya ce mutane da dama suna kuskuren danganta nasara da iko ga ’yan adam, maimakon su gane cewa Allah ne kaɗai ke juya al’amuran yadda Ya so.

“Sau da yawa a rayuwarmu muna danganta abubuwa ga mutane, alhali su ma halittu ne kawai,” in ji Sanusi.

“Idan ka tuna cewa yanayin rayuwa ba ya dawwama, kuma Allah ne ke sauya al’amura, hakan zai taimaka maka ka jure kuma ka daidaita halayenka.”

Ya gargaɗi mutane da kada su ƙasƙantar da kansu domin neman yardar masu iko.

A cewarsa, wasu mutanen kan ƙasƙantar da kansu ne saboda tunanin cewa wani mutum ne ke da iko a kan makomarsu.

Sanusi II, ya kafa misali da rayuwarsa domin nuna yadda al’amura ke sauyawa cikin ƙanƙanin lokaci.

Ya ce: “An dakatar da ni daga muƙamin Gwamnan Babban Banki, bayan watanni uku kuma na zama Sarki. Bayan wasu shekaru aka sauke ni daga sarauta, amma bayan shekaru huɗu na sake dawowa.

“Yanzu ina cikin fada, a kan karagar mulkina… A ƙarshe dai, dogaro ga Allah ne ke yin komai. Kada ka firgita.”

Ya ƙara da cewa lokacin da yake rayuwa bayan fitar da shi daga Kano, ya ba shi damar mayar da hankali kan karatu da kuma bunƙasa ci gaban gobensa.

Sanusi II, ya riƙe muƙamin Gwamnan CBN daga shekarar 2009 zuwa 2014.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne, ya tsige shi daga karagar mulki a shekarar 2020.

Sai dai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dawo da shi kan Sarautar Kano a shekarar 2024.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *