Yadda matashi ya kashe mutum 3 a massallaci a Abuja
[ad_1]
Wani matashi ya kashe mutum uku a yayin da suke jiran Sallar Asuba a wani masallaci da ke yankin Gwarimpa a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Matashin ya daɓa wa mai kula da masallacin da wasu mutum biyu wuƙa har lahira a yayin da suke jiran sallar a masallacin da ke Kado Bimko a shiyyar First Avenue da ke shararriyar unguwar.
Wani ganau, Muhammad Auwal, mai shago a kusa da masallacin, ya ce wanda aka fara kashewa, Alhaji Wanzam, dattijo ne da ke yin aski a kusa da masallacin.
“Alhaji Wanzam yakan iso masallaci tun ƙarfe 4 na asuba daga gidansa da ke kusa, ya buɗe masallacin, ya tsabtace harabar gaba ɗaya. Yana cikin aikin tsabtacewar ne, sai wanda ake zargi ya kai masa hari, ya yi ta daɓa masa wata sharɓeɓiyar wuƙa,” in ji Auwal.
Muhammad Auwal, ya shaida wa wakilinmu cewa wanda aka fi sani da Laminde Boka, bayan ya kashe Alhaji Wanzam, ya ci gaba da far wa wasu mutane da wuƙar da ke hannunsa.
Wanda ake zargin, wanda ake kyautata zaton yana cikin maye ya kuma daɓa wa wani mutum da ya yi ƙoƙarin tsayawa ya fuskance shi, wuƙa. Mutumin, wanda ke da injin nika a kasuwar da ke kusa, ya rasu a kan hanya yayin da ake ƙoƙarin kai shi asibiti.
Daga bisani, wanda ake zargi ya bi wasu masu ibada, ya cimma wani da ya faɗi ƙasa, ya daɓa masa wuƙa har lahira.
Daga bisani mutane suka kulle harabar masallacin, suka fara jifan wanda ake zargi da duwatsu, kafin daga ƙarshe su buge shi da sanda, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take.
Auwal ya ce a ranar aka tafi da gawar Alhaji Wanzam aka kai ta garinsu Gezawa a Jihar Kano a ranar, yayin da gawar na biyun aka kai Jihar Katsina.
Gawar wanda na uku, wanda birkila ne daga Jihar Gombe, an kai ta ɗakin ajiyar gawa a Asibitin Kubwa a Abuja, saboda ba a samu danginsa ba har zuwa ranar Lahadi, amma al’umna su san shi a matsayin ma’aikaci.
Wani shaida ya ce an fara jefar da gawar wanda ake zargi a kan juji, kafin daga bisani ’yan sanda su kai ta ɗakin ajiye gawar Asibitin Kubwa.
Mai unguwar Kado Bimko, Malam Ibrahim Isiaku, ya bayyana cewa bayan faruwar lamarin, masu ibada da suka saba yin barci a masallaci da kuma masu zuwa Sallar Asuba sun tsere zuwa sashen ƙauyen da yake zaune, inda suka yi sallah tare da su. Masallacin da abin ya shafa kuma an rufe shi.
Ya ƙara da cewa an gudanar da taro bayan lamarin, inda aka haɗa kwamitin masallacin, shugabannin kasuwar da ke kusa, da manajan tashar mai da ke gefen masallacin.
An cimma matsaya cewa daga yanzu ba za a ƙara bari kowa ya kwana a harabar masallaci ba, kuma duk wanda ya karya wannan umarni za a kai rahotonsa ga ’yan sanda domin a kama shi.
Ƙoƙarin wakilinmu na jin ta bakin DPO na Gwarimpa bai yi nasara ba, domin an ce ba ya ofis lokacin da wakilinmu ya kai ziyara jiya.
Sai dai wani babban jami’in ‘yan sanda ya tabbatar da faruwar lamarin.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link