An gano kabarin da ya haura shekara 1,000 cike da zinare a Panama
[ad_1]
Masana binciken tarihi wato archaeologists a harshen Ingilishi, sun gano wani kabari da ya haura sama da 1,000 a ƙasar Panama, wanda ke ɗauke da gawawwakin mutane tare da kayan ado na zinariya da na yumɓu.
An gano kabarin ne a wurin tarihi na El Cano da ke yankin Nata, kimanin kilomita 200 kudu maso yammacin birnin Panama.
Tun fiye da shekaru 20 da suka gabata masana sun ce ana tono wurin, wanda aka riga aka gano ɓurɓushin gawawwakin al’ummomin da suka rayu a yankin tun kafin zuwan Turawa.

A cewar masaniyar binciken tarihi, Julia Mayo, an samu ƙasusuwan mutane ne a cikin kabarin, suna zagaye da kayan zinariya da tukwane na yumɓu masu zane-zanen gargajiya, abin da ke nuna cewa mutanen da aka binne su na da matsayi mai girma a al’ummar su.
Kamar yadda jagorar binciken ta shaida wa AFP a ranar Juma’a, ta ce an gina kabarin ne tsakanin shekarun 800 zuwa 1000 bayan haihuwar Almasihu.
Ta ƙara da cewa, “Mutumin da aka binne tare da kayan zinariya shi ne mafi girman matsayi a cikin rukunin.”
Rahoton ya nuna cewa an same shi da awarwaron hannu guda biyu, ’yan kunne guda biyu, da kayan ado a ƙirji da ke ɗauke da siffofin jemagu da kada.
Wurin binciken tarihi na El Cano na da alaƙa da al’ummomin da suka rayu a tsakiyar lardunan Panama tsakanin ƙarni na 8 zuwa na 11. “A nan ne suke binne mamatan su tsawon kusan shekaru 200,” in ji Mayo.
Ta ce tuni aka gano wasu kaburbura guda tara makamancin wannan a wurin kafin wannan sabon binciken.
Ma’aikatar Al’adu ta Panama ta bayyana wannan lamarin a matsayin “mai matuƙar muhimmanci ga binciken tarihin Panama da fahimtar al’ummomin da suka rayu a yankin tsakiyar Amurka kafin zuwan Turawa.”
Masana sun ce irin waɗannan bincike na nuna cewa a wancan lokaci, mutuwa ba ta nufin ƙarshen rayuwa ba, illa wata hanya ce ta sauyawa zuwa wani mataki, inda har yanzu matsayi da darajar mutum ke da muhimmanci a al’umma.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link