Hasashe Game Da Siyasar Nijeriya A 2027

[ad_1]

Nan da shekara mai zuwa, wato 2027, Nijeriya za ta gudanar da zaɓe, wanda a tarihin kasar kamar ba a taɓa irinsa ba.

Jam’iyya mai mulki ta APC, ta shirya haɗiye duk fitattun ‘yan siyasa da suka yi shura da adawar APC, inda da yawa daga cikin masu rike da kujerun siyasa a jam’iyyoyin adawa ke rige-rigen sauya sheƙa zuwa APC.

Amma ko me hakan ke nufi, ko dai talala suke yi wa jam’iyyar daga karshe su gudu su barta?

A ɓangare guda kuma, gamayyar wasu shugabannin siyasa masu adawa, sun haɗe a sabuwar jam’iyyar adawa ta ADC don tunkarar zabe mai zuwa, inda Kwankwaso kuma na Jam’iyyar NNPP ya jaddada cewa, yana da ƙwarin gwiwa zai lashe zaɓen dake tafe ba tare da ya sauya jam’iyya ba.

Bari mu yi dubawa kan wasu fitattun ‘yan siyasa a 2027.

Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso

Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso fitaccen ɗan siyasa ne, wanda aka san shi da tasirinsa a siyasar Jihar Kano da kuma kafa ƙungiyar Kwankwasiyya da ke da ɗimbin matasa magoya bayan ɗan siyasar.

Kwankwaso ya shiga siyasa tun a jamhuriya ta Uku (1992–1999), inda aka zaɓe shi a matsayin Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano a 1992. Daga nan kuma, sojoji suka karɓi mulkin ƙasa wanda hakan ya dakatar da siyasarsa har sai da aka dawo mulkin farar hula (dimokuraɗiyya) a 1999.

Kwankwaso ya zama Gwamnan jihar Kano na farko a karkashin Jam’iyyar PDP bayan mulkin soji a shekarar 1999–2003. A lokacin mulkinsa, ya mai da hankali kan ilimi, kayayyakin more rayuwa, da ci gaban karkara, amma ya sha kaye a zaɓen da aka sake yi a 2003 sannan kuma ya sake lashe zaɓen Gwamna karo na biyu a 2011–2015.

Har ila yau, bayan ya cika wa’adin da kundin tsarin mulki ya tanadar masa na zama a kujerar Gwamna shekaru takwas kacal, Kwankwaso ya lashe zaɓen kujerar Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya a 2015-2019.

An naɗa Kwankwaso a matsayin Ministan Tsaro (2003–2007) a ƙarƙashin Shugaba Olusegun Obasanjo bayan ya yi rashin nasara a hannun Malam Ibrahim Shekarau bayan zangonsa na farko kan kujerar Gwamnan Kano.

Asali babban jigo ne a PDP. Ya kuma zama babban mamba da suka kafa Jam’iyyar APC a 2013. Daga baya ya koma PDP, kuma a 2022, ya koma Jam’iyyar NNPP inda ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP a babban zaɓen 2023. Ya samu ruwan kuri’u, musamman a Jihar Kano.

A shirye-shiryen zaɓen 2027 da ke tafe, Kwankwaso yana ci gaba da tallata burinsa na siyasa, duk da cewa, babu wata sanarwa a hukumance, amma ana raɗe-raɗin yana taka rawar gani a cikin siyasar Nijeriya wanda ke sa shi watakila ya yi rashin tabbas a siyasar 2027.

Yayin da Atiku da Obi suka sauya sheka zuwa ADC, Kwankwaso ya ci gaba da zama jam’iyyar NNPP a matsayin tsani mai karfi, ya ki shiga kowace hadakar jam’iyyun adawa.

A makon jiya, a ranar 20 ga Disamba, 2025, ya shirya babban taron NNPP a Abuja, inda ya yi alfahari cewa NNPP ita ce jam’iyyar mafi daidaito da tsara a Nijeriya. Ya jaddada cewa burinsa na lashe zaben shugaban kasa a 2027, ba tare da zama dan takarar mataimakin shugaban kasa ga Atiku ko wani ba.

Ahmed Tinubu ball

Bola Ahmed Tinubu fitaccen ɗan siyasa wanda aka fi sani da “ɗan fafutuka”, gina jam’iyya, sannan kuma yanzu, a matsayin shugaban ƙasa.

Ya fara siyasa a farkon shekarun 1990 a lokacin gwagwarmayar dimokuradiyya.

Ya zama babban jigo a cikin ƙungiyar masu fafutukar dimokuradiyya da ke adawa da mulkin soja bayan soke zaɓen 12 ga Yuni, 1993.

An zaɓi Tinubu a matsayin Sanata mai wakiltar Yammacin Legas a ƙarƙashin Jam’iyyar SDP a cikin ɗan gajeren lokaci na Jamhuriya ta Uku, inda aka katse jamhuriyar sakamakon ƙwace mulkin da sojoji suka yi a 1993.

Tinubu ya yi Gwamnan Jihar Legas a 1999–2007. Ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa Jam’iyyar APC a 2013, wacce ta tattaro jam’iyyun adawa da dama.

Ya fafata a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na APC kuma ya yi nasara.

An zaɓe shi a matsayin shugaban Nijeriya a watan Fabrairun 2023, ya kama aiki a ranar 29 ga Mayu, 2023 har zuwa yau.

Bayan ya samu tikitin kai tsaye na jam’iyyarsa ta APC a fafatawar zaɓen 2027 don ya sake tsayawa takarar shugaban kasa karo na biyu, shekarar 2026 za ta kasance shekara mai matukar muhimmanci ga Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ganin cewa, itace jajibirin shekarar zaɓe. Lokacin mulkinsa na farko, an fuskanci kalubale na kunci da tsadar rayuwa biyo bayan cire tallafin man fetur da kuma kaddamar da wasu sauye-sauye a fanni tattalin arziki da nufin ɗaga darajar Naira.

Don haka, Mutane za su so ganin yadda zai sarrafa sakamakon wadannan manufofi masu tsauri ta hanyar yakin nema zabe. Zuwa farkon shekarar 2026, matsin tattalin arziki da ake fuskanta za su zama makamin siyasa mafi karfi a kasar nan. A al’ada, ‘yan Nijeriya suna kada kuri’asu ne bisa lura da asalin kabila da yanki, amma 2026 na iya nuna wani sauyi zuwa zaben da ake yin sa bisa kwazon gwamnati wajen samar da ababen more rayuwa.

…. za mu ci gaba a mako mai zuwa

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *