Cinikin Waje Na Sin Ya Karu Da Kashi 3.8 Cikin Dari A 2025
[ad_1]
Bayanan da babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa cinikin waje na kasar ya karu da kashi 3.8 cikin dari a mizanin kowace shekara a bisa ma’aunin Yuan a shekarar 2025.
A cewar hukumar, a shekarar 2025, cinikin waje na kasar ya kai yuan tiriliyan 45.47, kimanin dala tiriliyan 6.48 na Amurka.
Cinikin waje na kasar Sin ya ci gaba da samun bunkasa a cikin shekaru tara a jere tun daga shekarar 2017.
Kazalika, kasuwancin waje na kasar Sin ya karu da kashi 6.1 cikin dari a mizanin kowace shekara zuwa yuan tiriliyan 26.99 a bara, yayin da cinikin shigo da kaya ya karu da kashi 0.5 cikin dari zuwa yuan tiriliyan 18.48 a bara, kamar yadda bayanan suka nuna. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link