Mutum 23 sun mutu a hare-haren ƙunar-baƙin-wake a Maiduguri
[ad_1]
Rundunar ‘yan sanda a Jihar Borno ta tabbatar da cewa mutane 23 sun mutu yayin da 108 suka jikkata sakamakon fashewar bama-bamai guda uku a lokaci guda a sassan Maiduguri.
Kakakin Rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargi da kai hare-haren ‘yan ƙunar bakin wake ne da suka yi amfani da na’urorin fashewa na gida.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan ya ce ana tunanin hare-haren ƙunar-baƙin-wake ne suka haddasa tashin bama-baman.
Sai dai ya ce abubuwa sun koma yadda ake a da a wuraren, yana mai kira ga mutane su bai wa ‘yan sanda rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba.
Aminiya ta ruwaito cewa, an samu fashewar bama-baman ne jim kaɗan bayan buɗa-baki a wurare daban-daban na birnin ciki har da kasuwar Monday Market da ofishin kiran waya da aika sakonni na Post Office da kuma Asibitin Koyarwa na Maiduguri.
Wani jami’in Hukumar NEMA mai ba da agajin gaggawa, Surajo Abdullahi, ya shaida wa Aminiya cewa mutum aƙalla 23 ne suka mutu sannan mutum 169 suka jikkata a hare-haren.
“A halin yanzu mutum 108 suna samun kulawa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, kuma 20 suna Asibitin Tunawa da Umaru Shehu yayin da mutum 17 ke Asibitin Ƙwararru na Maiduguri,” in ji shi.
Mazauna Maiduguri da dama sun ce a shekarun baya birnin ya fara mantawa da hare-haren bama-bamai da harbe-harben bindigogi amma yanzu lamura sun soma dagulewa.
“Komai ya dawo sabo yanzu – muna cikin tsoro da fargaba. Waɗannan hare-hare sun nuna yadda birnin na Maiduguri ke sake fama da tashin hankula bayan sun lafa a shekarun baya,” in ji wani mazaunin birnin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link