Sin Ta Bayyana Tsare-tsaren Zamanantar Da Noma Da Raya Yankunan Karkara
[ad_1]
Kasar Sin ta bayyana “kundinta mai lamba ta 1” na shekarar 2026 a yau Talata, inda ta bayyana tsare-tsaren bunkasa zamanantar da noma da yankunan karkara da kuma inganta raya karkara a dukkan fannoni.
Kundin an yi masa taken “Ra’ayoyin kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin da majalisar gudanarwar kasa a kan jagorantar zamanantar da noma da yankunan karkara da kuma kakkarfar inganta cikakkiyar raya karkara”.
Cikakken rubutun kundin ya kunshi sassa shida, wadanda suka hada da: inganta cikakken karfin samar da kayayyaki da aikin gona mai inganci, da aiwatar da tsarin tallafi na yau da kullum da kuma wanda aka tsara takamaime, da habaka ci gaban samun kudin shiga mai dorewa ga manoma, da bunkasa gina karkara mai saukin gudanar da rayuwa, da kasuwanci da kyawun gani mai kayatarwa bisa yanayoyinsu, da karfafa yin kirkire-kirkire kan tsare-tsare da dabarun aiki, da kuma kyautata cikakken shugabancin jam’iyyar kan ayyukan kula da “noma, yankunan karkara da manoma”.
Wanda ya zamo bayanai na farko kan manufofin gwamnati da mahukuntan tsakiya na kasar Sin ke fitarwa a kowace shekara, ana ganin kundin a matsayin manuniyar manufofin da aka fi ba su fifiko. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link