Ƙungiyar Matasan Jihar Filato Ta Yi Zanga-Zanga Kan Ƙaruwar Rashin Tsaro

[ad_1]

Matasan Jihar Filato karkashin inuwar kungiyar ‘Coalition of Northern Zone Ethnic Nationalities’ da kuma ‘Plateau Youth Coalition’, a ranar Laraba sun hallara gidan gwamnatin jihar da ke Jos domin nuna adawa da hare-haren da ake ci gaba da kai wa al’ummomin karkara da sauran matsalolin tsaro da suka addabi jihar.

Masu zanga-zangar, wadanda suka taru a gaban gidan gwamnati, sun nuna matukar takaicinsu kan kisan gilla da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ke ci gaba da yi ba tare da ƙaƙƙautawa ba.

Sun koka da cewa, har ma jami’an tsaro ba su da cikakken tsaro a halin yanzu.

Da yake jawabi yayin zanga-zangar, daya daga cikin shugabannin kungiyoyin, Ezekiel Peter Bini, ya ce kungiyar ta dauki wannan mataki ne bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari ga jami’an tsaro a yankin karamar hukumar Kanam a makon da ya gabata, inda suka kashe kusan jami’ai 14.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *