NAFDAC ta kama jabun maganin maleriya na ₦1.2bn a Legas

[ad_1]



Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta kama jabun magungunan zazzaɓin cizon sauro (maleriya) da darajarsu ta kai sama da Naira biliyan ₦1.2bn a Legas.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a a shafinta na sada zumunta X, inda ta ce jami’anta sun kai samame a wani ɗakin ajiyar kaya da ke yankin Ilasa-Oshodi, inda aka gano katan 277 na jabun magungunan maleriya nau’in Malamal Forte.

NAFDAC ta ƙara da cewa, “Ta kama katan 277 na jabun magungunan zazzaɓin cizon sauro na Malamal Forte waɗanda kuɗinsu ya kai sama da biliyan ₦1.2, a wani ɗakin ajiyar kaya da ke unguwar Ilasa-Oshodi a Jihar Legas”.

A cewar Hukumar NAFDAC, an ɓoye magungunan da ba a yi wa rijista ba ne a cikin kwalaye masu masu rubutun Diclofenac Potassium 50mg da aka shigo da su ba bisa ƙa’ida ba daga kamfanin Shanɗi Tianyuan Pharmaceuticals Group da ke Ƙasar China. An ayyana magungunan a matsayin na bogi a don gujewa amfani da su.

Darakta-Janar ta Hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ta bayyana wannan samamen a matsayin wani mataki na murƙushe su.

“Wannan kama jabun magungunan wani ɓangare ne na ci gaba da ƙoƙarin da NAFDAC ke yi a faɗin ƙasar don kare lafiyar jama’a da kuma tabbatar da magunguna masu inganci ne kawai ’yan Najeriya ke amfani da su,” in ji ta.

Ta yi bayanin cewa hukumar ta ƙara sanya ido a tashoshin jiragen ruwa da ma’ajiyar kayayyaki a faɗin ƙasar nan, tare da yin aiki tare da sauran jami’an tsaro domin daƙile ’yan fasa kwauri da ke cika kasuwar da kayayyaki masu haɗari.

Adeyeye ya jaddada cewa, gwamnati na goyon bayan ƙarfafa yaƙin da hukumar ke yi da jabun magunguna.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Darakta Janar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta jaddada ƙudurin hukumar tare da cikakken goyon bayan fadar shugaban ƙasa da ma’aikatar lafiya ta tarayya, na kawar da jabun magunguna da marasa inganci daga Najeriya.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *