ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin




Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya.

Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja.

Ya ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025.

ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025.

A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da yajin aikin, don haka dukkanin malamai za su daina aiki a lokacin yajin aiki.

Wannan yajin aikin na zuwa ne duk da cewa har yanzu gwamnati da ASUU na ci gaba da tattaunawa don warware matsalolin da suka daɗe suna fama da su.

Wasu daga cikin matsalolinsu sun shafi batun albashi, kuɗaɗen alawus-alawus, da kuma yarjejeniyar da aka cimma tun shekarar 2009 tsakanin ɓangarorin biyu.

Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya bayyana a ranar Laraba cewa gwamnati na matakin ƙarshe na tattaunawa da ASUU da sauran ƙungiyoyi don warware matsalolinsu.

Ya kuma ce gwamnati ta riga ta fitar da Naira biliyan 50 don biyan haƙƙoƙin malaman da suka cancanta, yayin da aka sake sakin wasu Naira biliyan 150 a kasafin kudin 2025 domin biyan buƙatun jami’o’i.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *