Majalisar Jihar Ribas Ta Dakatar da Shirin Tsige Gwamnan Fubara

[ad_1]

Majalisar Dokokin Jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da Mataimakiyarsa, Ngozi Odu, bayan sa bakin da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi a lamarin.

An amince da matakin dakatarwar ne a zaman majalisar da aka koma a ranar Alhamis a Fatakwal, babban birnin jihar. Wannan na zuwa ne bayan majalisar ta fara shirin tsige su a zamanta na farko na shekarar 2026 kan zargin aikata manyan laifuka.

  • HOTUNA: Wike Ya Buɗe Gidan Rediyo Don Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu A Ribas
  • Fubara Ya Rushe Majalisar Zartarwa Ta Jihar Ribas

Daga cikin zarge-zargen da aka ambata akwai rushe ginin majalisar dokokin jihar da kuma kashe kuɗi ba tare da amincewar majalisa ba, da sauran batutuwa.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a fitar da cikakken bayani kan dalilan dakatar da shirin tsigen ba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *