Kano Pillars ta dakatar da Kocinta
[ad_1]
Hukumar gudanarwar Kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars ta dakatar da Babban Kocinta Ahmed Garba Yaro Yaro da bai ba da shawara ga Kocin, Ogenyi Evans, nan take.
Ta kuma nada tsohon kyaftin kuma Mataimakin Koci, Gambo Muhammad nan take, ya jagoranci lamuran fasaha na ƙungiyar. Mai horar da masu tsaron raga, Suleiman Shuaibu, zai taimaka masa, yayin da Koci Garzali Muhammad (Kusa) daga Junior Pillars zai ba da ƙarin goyon baya har sai an fitar da sabbin umarni.
Kungiyar ta dauki wannan mataki ne bayan abin da ta kira “rashin tagomashinta” a Gasar Firimiyar Najeriya (NPFL) ta 2025/2026 da ake ci gaba da yi.
Sanarwa da kulob ɗin ta fitar, hukumar gudanarwar ta ce an ɗauki matakin ne bayan nazarin yadda ƙungiyar ta yi rashin nasara a wasannin ta na baya-bayan nan.
Ta ce “Yanzu haka, ’yan wasan sun buga wasanni takwas, amma nasara biyu kacal suka samu a ciki, sun yi canjaras biyu, sannan kuma an doke su a wasanni huɗu.”
Kulob ɗin, wanda yana ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da suka fi rawar gani a tarihin ƙwallon ƙafa a Najeriya, yana fama da rashin daidaituwa a wannan kakar, abin da ke tayar da hankalin magoya baya da masu ruwa da tsaki kan jagorancin ƙungiyar.
Sanarwar ta tabbatar wa magoya baya cewa hukumar gudanarwar ta ci gaba da jajircewa wajen dawo da ƙungiyar kan turba da kuma dawo da dabi’ar ta ta samun nasara.
Kano Pillars, wadda aka fi sani da ‘Sai Masu Gida’, a halin yanzu tana can ƙasan teburin gasar ta NPFL, kuma tana fatan samun canji mai kyau yayin da kakar ke ci gaba.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link