Tawagar Wakilan JKS Ta Ziyarci Kasashe Da Dama Domin Gabatar Da Ruhin Cikakken Taro Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20
[ad_1]
Kwanan nan, tawagar wakilan jam’iyyar kwaminis ta Sin wato JKS ta ziyarci Burtaniya, Turkiyya, Masar, da sauran kasashe, inda ta gana da jami’an gwamnatoci da shugabannin jam’iyyun siyasa, tare da yin tarurruka na musamman don gabatar da ruhin cikakken taro na 4 na kwamitin kolin JKS na 20 ga sassa daban-daban.
Jami’ai daga kasashe da dama sun yaba da muhimmancin cikakken taron na 4 na kwamitin kolin JKS na 20 ga kasar Sin da ma duniya baki daya, sun kuma yi yabo kan kwanciyar hankali da tabbacin da ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ya kawo wa duniya, sannan suka bayyana fatansu na zurfafa hadin gwiwa mai amfanarwa tare da kasar Sin da kuma bunkasa dangantakar bangarorin biyu.
Wakilan kasashen waje sun jaddada cewa, ya kamata a yi amfani da damar da ci gaban kasar Sin mai inganci ya kawo a lokacin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15, da kuma karfafa hadin gwiwa mai amfanarwa ga juna.(Safiyah Ma)
[ad_2]
Source link