’Yan ƙungiyar asiri sun kashe ɗan sanda a Bayelsa
[ad_1]
Wasu da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne sun kashe wani ɗan sanda, mai suna Oboh Goodluck a kan titin OMPADEC da ke unguwar Amarata, a Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa
Rahotanni sun ce ɗan sandan yana sanye da kayan gida lokacin da lamarin ya faru da safiyar Talata, a kan hanyarsa ta komawa daga aiki.
An ce waɗanda suka aikata laifin sun yi ƙoƙarin ƙwace masa waya da wasu kayayyaki kafin su harbe shi har lahira.
Unguwar Amarata ta daɗe tana fama da rikicin ƙungiyoyin asiri tun watan Disambar bara, lokacin da ƙungiyoyi biyu suka fara faɗa da juna.
Wannan ya jawo fargaba da tashin hankali a yankin.
Da safiyar ranar Talata, wasu mazauna unguwar sun ce ’yan sanda ɗauke da makamai sun shiga unguwar, sun kai wa gidaje samame tare da yin harbi.
Hakan ya sa mutane da dama suka gudu daga gidajensu saboda tsoro.
Wani mazaunin yankin ya ce ’yan sanda sun fasa musu tagogi lokacin samamen, kuma jama’a na cikin tsananin fargaba.
Mutanen yankin sun roƙi gwamnati da jami’an tsaro su yi hankali wajen gudanar da aikinsu, domin kauce wa ƙarin tashin hankali.
Kakakin rundunar, DSP Musa Muhammad, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce ana ci gaba da bincike domin gano waɗanda suka yi kisan.
Mutanen Amarata na roƙon gwamnati da hukumomin tsaro su gaggauta ɗaukar mataki domin dawo da zaman lafiya da kare rayuka.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link