A soma duban watan Shawwal ranar Laraba — Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya umurci musulmai a Najeriya da su fara duban watan Shawwal daga gobe Laraba, 29 ga watan Ramadan 1447, wanda ya yi daidai da 18 ga Maris, 2026.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da fadar sarkin ta fitar a ranar Talata, 17 ga Maris, 2026, yayin da watan Azumi na Ramadan ke cika kwanaki 28 da kamawa.
A takardar da Farfesa Sambo Wali Junaid, Waziri Sakkwato kuma shugaban kwamitin bai wa Sarkin Musulmi shawara kan harkokin addini, ya fitar, an shawarci duk wanda ya ga watan da ya sanar da hakimi ko uban ƙasa mafi kusa ko kuma ta hanyar kira ga majalisar Sarkin Musulmi a lambobin waya kamar haka: 08037157100, 08066303077, 08035965322.
Watan Shawwal na cikin watannin Musulunci masu muhimmanci, inda ake ci gaba da ibadar azumi na wasu ƙayyadaddun kwanaki da da ake so musulmai su gudanar don samun rabo da tsira a gobe ƙiyama.